Yadda 'Yan Bindiga ke Hada Hadar Kudi Ta POS, an Kama Mai Taimaka Masu

Yadda 'Yan Bindiga ke Hada Hadar Kudi Ta POS, an Kama Mai Taimaka Masu

  • An kama wani dan kasuwa da ke sana’ar POS da sayar da kayan gyaran babura a Jihar Katsina bisa zargin taimaka wa wani jagoran ’yan bindiga
  • Wanda ake zargin mai suna Isiyaku Nasiru, an kama shi tare da wasu mutane uku a wurare daban-daban a jihar Katsina
  • Rahotanni sun ce binciken jami’an tsaro na iya bankado yadda ake zargin ana safarar kudi da kayan aiki zuwa ga kungiyoyin ’yan bindiga a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – An tsare wani mai POS da mai sayar da kayan gyaran babura a Karamar Hukumar Matazu ta Jihar Katsina, Isiyaku Nasiru, bisa zargin taimakawa Kachalla Muhammadu wajen sarrafa kudi har na miliyoyin Naira.

Jami’an Katsina State Security Watch Corps sun kama Nasiru tare da Abubakar Sayaya, Nura Baka Sati da Ubale Mai Cange.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: An tura fitacciyar yar TikTok gidan yari kan 'zagin' wani ɗan siyasa a Kano

Wajen wani mai POS
Wani mai POS yan kirga kudi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama mutanen ne a wurare daban-daban a jihar tsakanin ranakun Alhamis da Asabar.

Zargin da ake yi wa mai POS

Shugaban Karamar Hukumar Matazu, Shamsuddeen Muhammad Sayaya, ya tabbatar da kama mutanen, yana mai cewa ana zargin suna da alaka da hanyar sadarwar Kachalla Muhammadu.

Ya ce ana ci gaba da binciken wadanda ake zargin, inda bayanan da aka samu za su iya taimaka wa jami’an tsaro wajen gano tsarin da ake zargin ke taimaka wa ayyukan ta’addanci a yankin.

Ana zargin Nasiru da kasancewa wani bangare na tsarin hada-hadar kudi da ake amfani da su wajen kai kudi ga mutanen da ke sayen makamai da sauran kayayyakin da ake bukata.

Matazu ta shafe shekaru tana fuskantar kashe-kashe, satar mutane, raba jama’a da muhallansu da kuma durkushewar harkokin tattalin arziki.

Yadda ya fara POS

Bayanan da Trust Radio ya tattara sun nuna cewa Nasiru dan asalin Karamar Hukumar Mashi ne, wanda ya zo Matazu domin neman ilimin addinin Musulunci kafin daga bisani ya zauna a yankin tare da matarsa da mahaifiyarsa.

Kara karanta wannan

An saki sunayen jami'an NSCDC 20 da aka dakatar kan mutuwar mutum 37 a Neja

Daga baya ya fara sana’ar sayar da kayan gyaran babura da gudanar da harkar POS.

Wani mazaunin Matazu, Babangida Musa, ya ce Nasiru ya bar makarantar addini shekaru da dama kafin rasuwar malaminsa, sannan ya shiga harkokin kasuwanci.

A cewar wani bayanin tambayoyin da aka gudanar, ana zargin Nasiru ya karbi kudi a tsabar kudi daga Muhammadu ta hannun wani mutum mai suna Salmanu.

An ce daga nan ne aka tura kudin zuwa ga wani Musa Sani, wanda ake zargin ya kai kudin ga wani dillalin makamai domin sayen makamai da sauran kayayyaki.

Taswirar jihar Katsina
Taswirar jihar Katsina a Najeriya. Legit
Source: Original

An kuma yi zargin cewa Salmanu na kai wa Nasiru tsakanin N3m zuwa N5m a tsabar kudi a kullum, wanda yake amfani da shi wajen gudanar da hada-hadar POS.

Maboyar Kachalla Muhammadu

Sunan Kachalla Muhammadu ya sha fitowa a rahotannin hare-haren ’yan bindiga a Matazu da wasu al’ummomin da ke kewaye da yankin.

Jami’an tsaro sun kara mayar da hankali kan wuraren da ake zargin kungiyoyin masu aikata laifi ke amfani da su a matsayin maboya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

A yayin wani samame na Operation FANSAN YAMMA, sojoji sun kai farmaki kan wasu maboya da ake zargin suna kusa da Maharba da Karaduwa a Matazu.

Bayan wasu kwanaki, sojoji sun ce sun kashe wani da ake zargin dan bindiga ne mai suna “Smally”, wanda suka bayyana a matsayin mataimakin Muhammadu.

An dakatar da jami'an NSCDC

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti mai mutane 10 mai zaman kansa domin gudanar da bincike kan mutuwar mutane 37 a Neja.

Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da kuma bude ido kan mutuwar wadanda ake zargin masu hakar ma’adinan ne.

Rahotanni sun nuna cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar da sunayen jami’ai 20 da aka dakatar dangane da lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng