Sanata na Hannun Daman Kwankwaso Ya Sa Labule da Shugaban APC da Barau

Sanata na Hannun Daman Kwankwaso Ya Sa Labule da Shugaban APC da Barau

  • A karo na biyu a 'dan tsakaninnan, Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya gana da Sanata Rufai Hanga, daya daga cikin manyan Kwankwasiyya a Kano
  • Amma a wannan zaman, an hada har da mataimakin shugaban majalisar dattawa na kasa Sanata Barau I Jibrin a babban birnin tarayya Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da lamari ke kara tsami a tsakanin tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rufa'i Hanga da ke ganin an i masa ba dai-dai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – An gudanar da wata ganawa ta sirri tsakanin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fadi abin da zai hana Obi da Atiku buge Tinubu a 2027

Wannan zama da aka yi a ranar Lahadi 20 ga watan Yuli, 2026 ya kara rura wutar zargin cewa Sanatan zai iya sauya sheka ya rabu da tsohon abokin siyasarsa, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sanata Rufai Hanga ya gana da manyan APC
Sanata Rufa'i Hanga, Farfesa Nentawe Yilwatda da Barau Jibrin jim kadan bayan taron sirri a Abuja Hoto: Professor Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Yilwatda ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana Hanga a matsayin daya daga cikin manyan jagororin jam'iyyar NDC a jihar Kano.

Hanga, Barau da shugaban APC sun zauna

Jaridar Punch ta ruwaito a cewar shugaban APC, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan hadin kai, zaman lafiya da kuma ci gaban jihar Kano tare da bukatar shugabanni su hada kai domin anfani al'umma.

Ya ce:

"Na yi farin cikin ganawa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da Sanata Rufai Hanga, daya daga cikin fitattun jagororin NDC a jihar Kano."

Yilwatda ya kara da cewa:

"Mun yi tattauna wa ta fahimtar juna da mutunta juna, kuma ta fi karkata kan hadin kai da ci gaban jihar Kano."

Kara karanta wannan

Jagoran matasan Kwankwasiyya ya koma tafiyar Gwamna Abba, Dankabo ya yi martani

Shugabanni na da damar ganawa - APC

Farfesa Nentawe Yilwatda ya kuma ce shugabanni suna da alhakin tattaunawa, samar da fahimtar juna da kuma gina dimokuradiyya mai karfi.

A cewarsa:

"Makomar Najeriya za ta fi kyau idan muka fifita muradun 'yan kasa fiye da bambancin jam'iyyu, tare da yin aiki domin cigaban kowa."
Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa an akwai bukatar shugabanni su hada kai
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda Hoto: Professor Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Ko da yake babu wani bangare da ya bayyana cikakken abin da aka tattauna, ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun sauye sauyen siyasa a Kano, kuma zaman ya zo bayan Sanata Hanga ya tattauna da gwamna Abba Kabir Yusuf.

Rufai Hanga shi ne sanatan NDC kadai daga Kano, amma kwanan nan ya rasa tikitin sake tsayawa takarar Sanatan Kano ta Tsakiya bayan jam'iyyar ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, tikitin takarar 2027.

Hanga ya magantu kan koma wa APC

A baya, mun kawo labarin cewa Sanata daya tilo da ya rage wa NDC, Rufa'i Sani Hanga mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya ce tun daga kafuwar tafiyar Kwankwasiyya ya kasance mai biyayya gare ta har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: "Akwai kalubale kan tikitin Obi da Kwankwaso"

Sai dai ya bayyana cewa duk da makauniyar biyayya da ya yi, ya ji labari Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce ai shi na gida ne, saboda haka a yi hakuri kuma ya dauki duk wani abu da ya zo masa a haka.

Amma Sanatan ya bude kofar sauya sheka, inda ya bayyana cewa duk da ba shi da niyyar amsa wata gayyata a yanzu, amma akwai abin da zai kore shi a NDC tare da koma wa jam'iyyar da masoyansa su ke so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng