Gwamnatin Kano Ta Bude Kofar Sulhu tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso

Gwamnatin Kano Ta Bude Kofar Sulhu tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso

  • Gwamnatin Kano ta ce a shirye take ta yi sulhu da tsohon gwamna kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso
  • Kwamishina yada labarai, brahim Waiya ya ce suna kallon Kwankwaso a matsayin uba kuma za ta yi marab da duk wani yunkuri na dawo da alakar da ke tsakaninsu
  • Sai dai har yanzu ba a sanar da wata yarjejeniya ta hukuma tsakanin Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf a shirye take ta yi sulhu da jagoran Kungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso.

Gwamnatin Abba ta bayyana cewa tana kallon tsohon gwamnan a matsayin uba, don haka za ta marabci duk wani yunkuri na dawo da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi rashi," Ododo ya yi alhini da aka tabbatar da rasuwar tsohon gwamna a Najeriya

Gwamna Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano tare da tsohon ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Waiya ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a wata tattaunawar wayar tarho da Leadership, yayin da yake martani kan kalaman da Kwankwaso ya yi cewa kofarsa a bude take domin sulhu da Gwamna Abba.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira dda aka yi da shi, inda ya ce bai yi watsi da Abba ba, kuma bai taba neman su rabu ba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Ya ce har yanzu yana kaunar gwamnan, yana mai cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya hana sulhu ba.

Gwamnatin Kano ta bude kofar sulhu

Da yake martani kan lamarin, Ibrahim Waiya ya ce :

“Mun dauki Dr Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin uba a gare mu. Don haka, kamar yadda ya ce kofarsa a bude take ga sulhu, tamu kofar ma a bude take."

Kwamishinan ya kara da cewa a baya Gwamna Abba ya bukaci magoya bayansa da kada su dauki Kwankwaso a matsayin abokin gaba.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kwankwaso ya yi maganar yafewa Gwamna Abba

“Bugu da kari, Gwamnanmu, Mai Girma Abba Kabir Yusuf, ya ce bai kamata mu yi fada da shi ba, domin uba ne a gare mu.
“Saboda haka, ba mu da wata matsala da sulhu idan har ya faru. Bugu da kari, ba fada ba ne a zahiri; kawai bambancin ra’ayi ne,” in ji shi.

Dalilin rabuwar Abba da Kwankwaso

Wadannan kalamai sun biyo bayan rashin jituwar siyasa da ta kunno kai tsakanin Abba da Kwankwaso bayan gwamnan ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Abba, wanda ya kasance abokin siyasar Kwankwaso kuma mabiyinsa, ya zama dan takarar NNPP na gwamnan Kano a zaben 2023 tare da goyon bayan tsarin siyasar Kwankwasiyya.

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnati Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Daga bisani, sauya shekar Abba zuwa APC ya sauya alakar siyasa tsakaninsa da Kwankwaso, tare da sauya yanayin siyasar Kano gabanin babban zaben 2027.

Duk da cewa Kwankwaso ya nuna aniyarsa ta yin sulhu, har yanzu shi da Gwamna Abba ba su sanar da wata yarjejeniya da za ta dawo da alakarsu ta siyasa ba.

Abin da Kwankwaso ya fada kan sulhu

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya cire Atiku cikin wadanda ya kamata su nemi shugaban kasa

Tun farko, kun ji cewa Kwankwaso ya ce a shirye yake ya sasanta da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, idan gwamnan ya nuna bukatar hakan.

Kwankwaso ya ce ba ya rike da gaba, yana mai cewa ya taba yafewa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje duk da rashin jituwar da ta taba farraka tsakaninsu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262