'Yan Qadiriyya Sun Yi Matsaya kan Tazarcen Tinubu, Za Su Fara Addu'o'i
- Jagoran Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin wa’adi na biyu
- Ya ce nadin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC ya ƙara ƙarfafa alaƙar ƙungiyar da yaƙin neman zaɓen
- Sheikh Qaribullah ya ce Qadiriyya za ta fara addu’o’i ga Tinubu, musamman kan zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kawo ƙarshen rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jagoran ƙungiyar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin neman wa’adi na biyu a ofis.
Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2026, lokacin da ya karɓi tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu da Sanata Abdul’aziz Yari ya jagoranta.

Source: Facebook
Nadin Yari ya ƙara ƙarfafa alaƙa
Jagoran Qadiriyya ya ce nadin Yari a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC ya ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙungiyar Qadiriyya da tawagar yaƙin neman zaɓen, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce Sanata Abdul'azizi Yari ya kasance yana da kusanci da ƙungiyar sama da shekaru 20.
Sheikh Qaribullah ya ce:
“Fiye da shekaru 20 muna tare da Abdul’aziz Yari, kuma ya kasance yana nuna goyon bayansa ga wannan gida. Yana daga cikinmu, kuma duk abin da ya zo da shi, ba mu da wani zaɓi face mu goyi bayansa.”
Qadiriyya ta ce tana goyon bayan Tinubu
Malamin ya ce ƙungiyar ba wai goyon bayan neman sake zaɓen Tinubu kaɗai take yi ba, har ma tana ganin Shugaban yana da “kyakkyawar manufa” ga Najeriya.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar Qadiriyya za ta fara gudanar da addu’o’i ga Shugaba Tinubu, inda za a mai da hankali kan zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kawo ƙarshen rashin tsaro.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: An bankado yadda aka bayar da cin hancin N650m don tazarcen Obasanjo
"Za mu fara addu’o’i tare da dukkan mabiyanmu. Addu’o’in za su mayar da hankali kan zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga dimbin matasanmu.” In ji shi.
Za su yi addu’ar kawo ƙarshen rashin tsaro
Sheikh Qaribullah ya bayyana fatan cewa idan Tinubu ya samu damar shiga wa’adi na biyu, Najeriya za ta samu sauƙi daga matsalar rashin tsaro.
"Muna fatan yayin da zai shiga wa’adinsa na biyu, Najeriya za ta fita daga cikin ƙuncin rashin tsaro.” In ji shi.
Tawagar Yari ta ziyarci shugabannin addini
Sanata Abdul’aziz Yari ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da James Faleke, Sanata Ali Modu Sheriff, Aminu Masari da Adamu Aleiro, tare da wasu mambobin tawagar yaƙin neman zaɓen.
Yari ya ce tawagar ta fara gudanar da ganawa da shugabannin addinai ne saboda irin girman mutuncin da take yi musu.

Source: Facebook
Tinubu ba zai je taron UNGA ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu, ba zai je babban taron majalisar dinkin duniya (UNGA) ba.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa, Kashim Shettima, da ya wakilce shi a wajen taron wanda za a yi a Amurka.
Asali: Legit.ng
