NiMet: Ruwan Sama zai Barke a Gombe, Kano da Jihohi Kusan 30

NiMet: Ruwan Sama zai Barke a Gombe, Kano da Jihohi Kusan 30

  • Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar daga Litinin zuwa Laraba
  • Hukumar ta ce a wasu wuraren, iska mai ƙarfi na iya tasowa kafin fara tsawa da ruwan sama, inda ta buƙaci jama'a su ɗauki matakan kariya
  • Hasashen ya shafi yankunan Arewa, Arewa ta Tsakiya da Kudancin Najeriya, tare da bayyana jihohin da ake sa ran samun ruwan sama a ranakun uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen tsawa da ruwan sama a sassa daban-daban na Najeriya daga Litinin zuwa Laraba.

Hukumar ta fitar da hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, inda ta yi gargadin cewa iska mai ƙarfi na iya tasowa kafin tsawa a wasu wuraren da ake sa ran samun ruwan sama.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga ke hada hadar kudi ta POS, an kama mai taimaka masu

Yadda ake ruwan sama
Wani waje da ake ruwa da iska. Hoto:Getty Images
Source: Original

Hasashen yanayi na yau Litinin

NiMet ta wallafa a X cewa a safiyar Litinin, za a yi tsawa mai haɗe da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Taraba da Kebbi.

Daga baya da rana ko da yamma, ana sa ran samun tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan Arewa maso Gabas, Kaduna, Taraba da Kebbi.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, hukumar ta ce za a samu tsawa mai haɗe da ruwan sama kaɗan a wasu sassan Jihar Neja da safe.

Daga baya da rana ko da yamma, ana sa ran samun tsawa tare da matsakaicin ruwan sama a mafi yawan sassan yankin.

A kudancin ƙasar, NiMet ta yi hasashen kasancewar sararin sama cike da gajimare a safiyar Litinin, tare da tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu sassan Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.

Za a yi ruwa ranar Talata

A ranar Talata, NiMet ta yi hasashen samuwar gajimare a wasu sassan Arewa da safe, tare da tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu sassan Taraba.

Kara karanta wannan

Wakilan Tinubu sun je gidan Dahiru Bauchi, sun gargadi 'yan Arewa kan 2027

Daga baya da rana ko da yamma, ana sa ran tsawa mai haɗe da matsakaicin ruwan sama a mafi yawan sassan yankin Arewa.

Punch ta wallafa cewa a Arewa ta Tsakiya, hukumar ta ce za a samu sararin sama mai ɗan gajimare da safe.

Daga baya kuma ana sa ran tsawa da matsakaicin ruwan sama a wasu sassan Abuja, Neja, Nasarawa da Plateau.

A kudancin ƙasar, NiMet ta yi hasashen kasancewar gajimare a mafi yawan sassan yankin da safe, kafin samun tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu sassan Ebonyi, Enugu, Abia da yankin Kudu maso Kudu.

Ana ruwan sama a Najeriya
Yadda me Napep ke tafiya ana ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hasashen ruwa a ranar Laraba

A ranar Laraba, hukumar ta yi hasashen sararin sama mai ɗan gajimare a sassan Arewa, tare da tsawa da matsakaicin ruwan sama a jihohi da dama da safe.

Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Borno, Bauchi, Gombe, Kaduna, Adamawa da Taraba.

NiMet ta kuma yi hasashen tsawa mai haɗe da matsakaicin ruwan sama a mafi yawan sassan Arewa daga baya da rana.

Kara karanta wannan

Bidiyon Aisha Buhari, Dino Melaye, Seyi Tinubu da wasu suna liyafa a Spain

A Arewa ta Tsakiya, ana sa ran samun sararin sama mai ɗan gajimare da safe, tare da tsawa da ruwan sama kaɗan a wasu sassan Abuja, Plateau, Neja da Nasarawa.

An yi sabon gargadi kan ambaliya

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya, NIHSA, ta yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa mai tsanani a jihohi 15 daga 19 zuwa 25 ga Satumba 2026.

Hukumar ta buƙaci mazauna al'ummomin da ke cikin haɗarin ambaliya da su koma wuraren da suka fi tsayi da aminci domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Daraktan Janar kuma Babban Jami'in Gudanarwa na hukumar, Umar Mohammed, ya ce ana sa ran hauhawar ruwan koguna za ta haifar da ambaliya a wasu al'ummomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng