Kurunkus: An Fitar da Cikakken Jerin Sunayen Matasa 37 da Suka Mutu a Hannun NSCDC

Kurunkus: An Fitar da Cikakken Jerin Sunayen Matasa 37 da Suka Mutu a Hannun NSCDC

  • An bayyana sunayen matasa 37 da suka rasa rayukansu a dakin ajiyar masu laifi na hukumar tsaro ta NSCDC da ke jihar Neja
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta dauki matakin bincike don gano abin da ya faru wanda ya kai ga mutuwar matasa fiye da 30
  • Hukumar NSCDC ta kama wadannan matasa ne bisa zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - A makon da ya gabata ne hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta tabbatar da mutuwar wasu matasa 37 da ta kama bisa zargin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a jihar Neja.

Lamarin da ja hankalin mutane daga sassa daban-daban a Najeriya, inda wasu ke zargin akwai sakacin jami'an tsaron gwamnatin Najeriya a mutuwar wadannan matasa.

Kara karanta wannan

Ba za a yi haka ba: Kungiya ta yi martani kan kiran a kori shugaban NSCDC kan mutuwar matasa a Neja

NSCDC.
Jami'an hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya (NSCDC) a bakin aiki Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Wasu matakan da aka dauka

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakai domin gano duk mai hannu a lamarin, ciki har da dakatar da kwamandan NSCDC na Neja da kafa kwamitin bincike.

Haka zalika an dakatar da jami'an NSCDC da dama duk a wani mataki na tabbatar da an gudanar da bincike cikin gaskiya kuma a bayyane,

Yayin da ake dakon sakamakon bincike, an fitar da sunayen mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, wadanda suka mutu a hannun jami’an NSCDC a jihar Neja.

A halin da ake ciki, NSCDC ta kama tare da gabatar da jami’ai 24, ciki har da Kwamandan rundunar jihar Neja, Subaru Siyaka Aniviye, dangane da mutuwar masu hakar ma’adinan.

Sunayen wadanda suka mutu

Sunayen matasan da suka rasa ransu a dakin ajiyar wadanda ake zargi na NSCDC sun hada da:

  1. Ibrahim Sani
  2. Fahad Sa’adu
  3. Abdulsalam Ismail
  4. Usman Aliyu
  5. Abubakar Alhaji
  6. Sani Nasir
  7. Sanusi Khalid
  8. Ahmad Aliyu
  9. Safiyanu Abdullahi
  10. Suleiman Dantala
  11. Idris Haruna
  12. Sani Yakubu
  13. Safiyanu Abubakar
  14. Abdullahi Abubakar
  15. Abubakar Musa
  16. Abdul Mudassir
  17. Suleiman Lawal
  18. Usman Abdullahi
  19. Samuel Sambo
  20. Ibrahim Musa
  21. Yusuf Nasiru
  22. Umar Lawal
  23. Isyaku Amisu
  24. Bissallah Adamu
  25. Abdulbari Suleiman
  26. Shafisu Lado
  27. Usman Ahmad
  28. Usman Ibrahim
  29. Sani Isyaku
  30. Musa Ibrahim
  31. Idris Bashir
  32. Kabiru Suleiman
  33. Emmanuel Emeka
  34. Mu’awiya AbdulKarim
  35. Abdul Gafar Abubakar
  36. Usman Haruna
  37. Aro Salihu Soba

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta kama baƙin haure 14,782 cikin mako guda

An bayyana cewa Mu’awiya AbdulKarim, Abdul Gafar Abubakar, Usman Haruna da Aro Salihu Soba ba su cikin jerin sunayen da babban asibitin ya fitar.

NSCDC.
Kwamandan hukumar NSCDC na jihar Neja da aka dakatar da wasu jami'ai a bakin aiki Hoto: @Official_NSCDC
Source: Facebook

Matakin da Tinubu ya dauka

A wani kabarin, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gudanar da bincike na gaskiya kan mutuwar mutanen da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a hannun NSCDC.

Tinubu ya nuna matuƙar damuwa kan rahoton mutuwar mutanen, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban batu da ke buƙatar bincike cikin gaggawa da ɗora alhakin da ya dace.

Shugaban kasar ya kuma ce bai kamata wani ɗan ƙasa ya rasa ransa yana hannun gwamnati saboda sakaci, cin zarafi, rashin tausayi ko gazawar jami’i wajen sauke nauyin da ke kansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262