Rarara Ya Karbo Naira Miliyan 500, zai Shiga Arewa da Tawaga Tallata Tinubu

Rarara Ya Karbo Naira Miliyan 500, zai Shiga Arewa da Tawaga Tallata Tinubu

  • Wasu mambobin tafiyar Triple R sun yi bankwana da kungiyar bayan rikicin da ya taso kan rabon kudi da aka karbo daga 'yan siyasa
  • Rahoto ya nuna cewa sakataren kungiyar, Ahmed Bifa ya amince an karbi kudi amma ya musanta cewa kudin ne ya fi muhimmanci a tafiyar
  • Bifa ya bayyana cewa tsohon gwamnan Zamfara ya ba tafiyar kudi har Naira miliyan 500 domin tallata shugaban kasa Bola Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Tafiyar Tripple R da mawaki Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta ta fada cikin takaddama bayan wasu mambobin ta sun yanke shawarar barin kungiyar, suna zargin akwai rashin gaskiya wajen rabon kudi.

Rabiu Rikadawa, daya daga cikin wadanda suka yi bankwana da tafiyar, ya yi korafi yana mai cewa an sanya siyasa a lamarin maimakon cigaban Arewa.

Kara karanta wannan

Jirgin sama ɗauke da mataimakiyar shugaban ƙasa da wasu mutum 8 ya yi hatsari

Shugaban kasa Bola Tinubu da Rarara
Bola Tinubu a tsakiyar Rarara da Aisha Humaira. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Twitter

A wani bidiyo da DW ta wallafa a Facebook, Rikadawa ya fassara lamarin da cewa ana ganin tafiyar a matsayin wata hanyar tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Tinubu ne, ba domin amfanin talakawa ba.

Ahmed Bifa ya kare Rarara

A daya bangaren sakataren kungiyar, Ahmed Bifa, ya ce tun farko ba a kafa tafiyar kan kudin da za a karba ba, amma ya yarda babu yadda za a tafiyar ba tare da kashe kudi ba.

Bifa ya kuma yi tsokaci kan zargin da aka yi wa tafiyar na yin rawa a majalisar dokokin tarayya, yana mai cewa shugaban tafiyar Rarara mawaki ne tun asali, saboda haka ba laifi idan ya yi waka ko rawa a duk wani taro.

A wani sako na daba, DW Hausa ta wallafa a Facebook cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ba wa tafiyar kudi Naira miliyan 500 don tallata Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya

Martanin jama'a kan lamarin

Lamarin ya haifar da fushi rai a tsakanin 'yan Arewa a shafukan sada zumunta, inda Ibrahim Muazzam Lawan ya rubuta cewa:

"Gaskiya Allah ya isa tsakaninmu dai tunda kace kashe mutane agunka ba matsala ba ce."

Fadima Ibrahim ma ta ba da ra'ayinta inda ta ce:

"Wallahi dagaske ne, in gwamnati tana son cin zaɓe sai ta dakatar da wannan kungiya daga yi masu kamfen."

Ibrahim Usman Maryam ya soki Bifa kai tsaye yana cewa:

"Bifa wallahi da kana birgeni saboda mutuncinka da kamalarka amma wannan maganganun naka sun bata min rai,"

Abduljalil Maikarfe ya kara da cewa:

"Kai jama'a wannan kolon almajirin ya hargitsa hazo. Wai mutane da qimarsu amman sun zama 'yan abi yarima a sha kida."
Ahmad Bifa da ke aiki da Rarara
Sakataren kungiyar su Rarara, Ahmad Bifa. Hoto: Bifa Mohammed Adamu
Source: Facebook

Zayyad Nasir Abukur shi ma ya zuba ra'ayinsa mai tsawo inda ya ce duk wanda ya karbi kudi ya kawo bala'i da masifa ga al'umma, yana mai nuni da cewa matsalar ta yi zurfi musamman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi hasashen abin da 'yan adawa za su ce idan Tinubu ya ci zaben 2027

Rarara ya caccaki Davido

A wani labarin, mun kawo muku cewa mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya caccaki fitaccen mawaki Davido kan wata riga da ya sanya a Amurka.

Davido ya je wajen taron gasar cin kofin duniya a Amurka sanye da riga mai dauke da sunayen malamai da daliban da aka sace a jihar Oyo.

A kan haka Rarara ya masa kakkausar suka ya ce hakan tona asirin Najeriya ne a idon duniya, inda ya kuma yi zargin cewa Davido bai da kishin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng