Amurka na Fama da Kanta, Ta Amince da Sayar da Manyan Makamai ga Israila
- Kafofin watsa labaran Amurka sun ce gwamnatin Donald Trump na kan hanyar amincewa da yarjejeniyar makamai ta dala biliyan 2.8 ga Isra’ila
- Tarin makaman ya ƙunshi bama-bamai 40,000 masu nauyin ton ɗaya, ciki har da MK-84, BLU-117 da I-2000 Penetrator
- Rahoton ya zo ne yayin da sojojin Amurka ke fuskantar ƙarancin makamai, bayan an karar dimbin makamai a yaƙi da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Gwamnatin Amurka ta shirya sayar da makamai masu yawa ga babbar kawarta Israila.
Gwamnatin ta Trump n kan hanyar amincewa da wani kunshin makamai da darajarsa ta kai dala biliyan 2.8 da za a sayar wa Isra’ila.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce kafafen yaɗa labaran Amurka suka ruwaito ranar Talata, 15 ga watan Satumban 2026.
Rahoton ya ce yarjejeniyar na ɗaya daga cikin manyan cinikayyar makamai da aka kulla cikin ’yan shekarun nan, inda aka shirya sayar da bama-bamai 40,000, kowannensu yana da nauyin ton ɗaya.
Manyan bama-bamai na cikin yarjejeniyar
Jaridar The Washington Post ta ce za a gudanar da cinikin ne da kuɗin masu biyan haraji na Amurka.
Ta ce kunshin ya ƙunshi wasu daga cikin manyan makaman da ake da su a rundunonin ƙasashen Yamma, ciki har da bama-bamai 20,000 MK-84, 20,000 BLU-117 da kuma 20,000 I-2000 Penetrator warheads.
A nata rahoton, The New York Times ta ce gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta amince da sayar da makaman, tana ambaton wani jami’in Amurka a matsayin majiyar bayanin.
Gwamnatin Amurka ta yi takatsantsan kan yarjejeniyar
Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa dukkan yarjejeniyoyin sayar da makamai ga ƙasashen waje suna bin tsarin da ya dace.
Sai dai jami’in ya ƙi yin ƙarin bayani kan yarjejeniyoyin da har yanzu ake kan aiwatar da su.
Haka kuma, wani mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce ma’aikatar ba ta tabbatarwa ko yin tsokaci kan shawarwarin sayar da makamai har sai an sanar da Majalisar Dokokin Amurka a hukumance.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000
Amurka na fuskantar ƙarancin makamai
Rahoton yarjejeniyar ya fito ne yayin da sojojin Amurka ke fuskantar ƙarancin wasu nau’ikan makamai.
An ce makaman Amurka na raguwa cikin sauri sakamakon yaƙin da Iran, yayin da gwamnatin Amurka ta kashe dala biliyan 22.3 wajen sayen makamai tsakanin 28 ga Fabrairu zuwa 30 ga Yunin 2026.
Trump ya riga ya amince da wasu makamai
A watan Fabrairun 2025, gwamnatin Trump ta amince da sayar wa Isra’ila makamai da kayan yaƙi da darajarsu ta haura dala biliyan 7.4, ciki har da bama-baman MK-84.
A baya, gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ta dakatar da jigilar wasu bama-bamai masu nauyin fam 2,000 zuwa Isra’ila saboda damuwar da ake da ita kan mutuwar fararen hula a Gaza.
Sai dai gwamnatin Trump ta amince da jigilar bama-baman bayan ta hau mulki a farkon shekarar 2025.

Source: Getty Images
Majalisar Amurka ta kada kuri'an kan yakin Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilan Amurka ta kada kuri’a kan kudirin da zai bukaci Shugaba Donald Trump ya janye sojojin Amurka daga arangama da Iran.
Kudirin ya samu kuri’u 220 na amincewa yayin da kuri’u 204 suka nuna adawa da shi. ‘Yan Republican 7 ne suka hada kai da ‘yan Democrat wajen amincewa da kudirin.
Asali: Legit.ng
