Rigima Ta Kunno Kai, An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC da Kwamishinan Jihar Kebbi
- APC ta dakatar da shugabanta na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Muhammad Kana-Zuru, da na karamar hukumar Zuru, Aliyu Abubakar Abiola
- Jam’iyya mai mulki ta ce ta dauki matakin ne bayan korafe-korafe daga masu ruwa da tsaki da kuma binciken cikin gida
- Gwamnatin jihar Kebbi ta kuma dakatar da Kwamishinan Kiwon Dabbobi da Kifi, Kabir Usman Alaramma Zuru nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi, Nigeria - Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ta dakatar da shugabanta na jiha, Alhaji Abubakar Muhammad Kana-Zuru.
Haka zalika jam'iyyar ta kuma dakatar shugaban APC na karamar hukumar Zuru da ke Kebbi, Aliyu Abubakar Abiola, lamarin da ke nuna alamun rikici ya mamaye jam'iyyar.

Source: Twitter
NTA News ta ruwaito cewa dakatarwar ta zo ne bayan zarge-zargen aikata wasu laifuffukan da suka shafi jam’iyya, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a siyasar jihar Kebbi
Dalilin dakatar da shugabannin APC
A wata sanarwa da sakataren jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Sa’idu Muhammad Kimba ya sanya qwa hannu, jam’iyyar ta bayyana cewa an dauki matakin ne bayan samun korafe-korafe daga masu ruwa da tsaki.
Sanarwar ta ce APC ta yi la’akari da rahotannin da aka samu kafin yanke shawarar dakatar da shugabannin biyu.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana cikakken irin laifuffukan da ake zargin shugabannin da aikatawa ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Gwamnatin Kebbi ta dakatar da kwamishina
A wani bangaren kuma, gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da dakatar da Kwamishinan Harkokin Kiwon Dabbobi da Kifi, Kabir Usman Alaramma Zuru, daga mukaminsa nan take.
Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Yakubu Bala Tafida ya fitar ta ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an bayar da wani sabon umarni.
Gwamnatin ta umarci kwamishinan da aka dakatar ya mika dukkan takardun ofis ga babban sakataren ma’aikatar domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.

Source: Facebook
An fara surutu a APC ta Kebbi
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnati ba ta bayyana dalilin dakatar da kwamishinan ba, yayin da ake sa ran za a fitar da karin bayani kan lamarin nan gaba.
Dakatar da manyan shugabannin APC da kuma kwamishinan gwamnati a lokaci guda ya janyo ce-ce-ku-ce a harkokin siyasa a jihar Kebbi musamman a jam'iyya mai mulki.
APC ta maida martani ga 'yan adawa
A wani rahoton, kun ji cewa Jam'iyyar APC mai mulki ta soki jam’iyyun adawa bisa goyon bayan kiran Bola Tinubu ya sauka daga mulki saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.
Daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da kiran Tinubu.ya yi murabus, yana mai bayyana kiran a matsayin rashin hankali da kokarin sanya siyasa a harkar tsaro.
Ya kafa hujja da cewa ba Najeriya ce kadai ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki ba, yana mai cewa ƙasashe kamar Amurka da Birtaniya ma suna fuskantar irin waɗannan ƙalubale.
Asali: Legit.ng

