Yan Daba Sun Farmaki Ofishin Jam'iyyar NDC, Sun Lalata Kayan Miliyoyi
- Wasu ’yan daba da ake zargin ’yan siyasa ne sun kai hari sakatariyar NDC inda suka lalata allunan talla da tutocin yakin neman zabe
- Dan takarar NDC na majalisar wakilai, Fugbara Ohaka, ya yi Allah wadai da harin, tare da kira ga ’yan jam’iyya su kwantar da hankali
- Ohaka ya bukaci hukumomin tsaro su binciki harin, gano wadanda suka aikata shi kuma su hukunta su, yana mai kira ga zaman lafiya gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers — Wasu ’yan daba da ake zargin ’yan siyasa ne sun kai hari sakatariyar NDC da ke jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Emohua a Rivers, inda suka lalata allunan talla, tutoci da sauran kayayyakin yakin neman zabe.

Source: Twitter
An ce lamarin ya faru ne a daren Laraba a sakatariyar jam’iyyar da ke garin Emohua, hedkwatar karamar hukumar, cewar Vanguard.
Maharan sun lalata alamomin jam’iyyar, ciki har da manyan allunan talla da tutocin yakin neman zabe da aka kafa a jikin ginin.
Dan takarar NDC na majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Ikwerre/Emohua, Hon. Fugbara Ohaka, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ohaka ya yi Allah wadai da harin, tare da yin kira ga ’yan jam’iyya da magoya bayanta su kwantar da hankali.
Ya ce bai kamata bambance-bambancen siyasa su rikide zuwa tashin hankali, tsoratarwa ko lalata kadarori ba.
Ya roki ’yan jam’iyya da magoya bayanta su kasance masu zaman lafiya tare da bin doka, yana mai cewa NDC ba za ta bari a tsokane ta ta dauki doka a hannunta ba.
Ohaka ya kuma bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan lamarin tare da gano wadanda ke da alhakin lalata kadarorin jam’iyyar.
A cewarsa, duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifin ya kamata ya fuskanci hukunci bisa tanadin doka.
Ohaka ya ce ya kamata siyasa ta mayar da hankali kan ra’ayoyi, ci gaba, hidima da jin dadin jama’a, maimakon tashin hankali da lalata kadarori.
Ya kara da cewa zabuka za su zo su wuce, amma alaka tsakanin mutane da al’ummomi za ta ci gaba da kasancewa.
Saboda haka, ya bukaci ’yan siyasa su rungumi zaman lafiya, hakuri da mu’amala mai kyau yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
Ya sake tabbatar da kudurinsa na gudanar da yakin neman zabe cikin zaman lafiya, bisa muhimman batutuwa da mai da hankali kan bukatun jama’a.
Ohaka ya kuma yi kira da a ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Emohua, Ikwerre, Rivers da Najeriya baki daya.
Yan daba sun tarwatsa kamfen APC
An ji cewa rikici ya barke a Ilesa, Osun, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan gangamin yakin neman zaben gwamnan APC.
Wani jigo a APC ya zargi ɗan majalisar jihar Olawale Akerele da jagorantar waɗanda suka kai harin, tare da neman a kama shi.
Sai dai Akerele ya musanta zargin, yana cewa jami’an tsaron Amotekun da ke tare da shi ne suka harba bindiga sama domin kare kansu.
Asali: Legit.ng

