Fada Ya Yi Zafi; Saudiyya Ta Gamu da Gagarumar Matsala bayan Kai Hari Mecca

Fada Ya Yi Zafi; Saudiyya Ta Gamu da Gagarumar Matsala bayan Kai Hari Mecca

  • Houthi ta ce dakarunta sun harbo jirgin yaƙin Saudiya kirar F-15 a sararin samaniyar Marib da makami mai linzami da aka kera a cikin gida
  • Kakakin sojojin ƙungiyar, Yahya Saree, ya ce jiragen yaƙin Saudiya sun kai hare-hare sama da 450 a wasu yankunan Yemen cikin makon nan
  • Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da kare sararin samaniyar Yemen da ikonta daga duk wani hari ko take hakkin 'yancin ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Sanaa, Yemen - Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta ce dakarunta sun harbo jirgin yaƙin Saudiya kirar F-15 a sararin samaniyar ƙasar, yayin da yake gudanar da wani samame na soji.

An bayyana cewa an kakkabo jirgin yakin na Saudiyya ne a sararin samaniyar lardin Marib na kasar Yemen.

An harbo jirgin Saudiyya a Yemen
Jirgin F-15 na Saudiyya a sararin samaniya Hoto: AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An harbo jirgin a Marib

Kara karanta wannan

Boye boye ya kare, Amurka ta bayyana gagarumar barnar da Iran ta yi mata

Kakakin rundunar sojojin Houthi, Yahya Saree, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton tashar Aljazeera.

Ya ce sojojin Yemen sun samu nasarar harbo jirgin ne da taimakon Allah, yayin da yake gudanar da ayyukan da ƙungiyar ta bayyana a matsayin hare-haren ƙiyayya.

“Dakarun sojin Yemen, da taimakon Allah da falalarsa, sun samu damar harbo jirgin yaƙin Saudiya kirar F-15 yayin da yake gudanar da ayyukan ƙiyayya kan mutanenmu,” in ji Saree.

Ya ƙara da cewa jirgin na taimakawa wajen ƙara yawan ayyukan sojin Saudiya a sararin samaniyar lardin Marib.

An yi amfani da makami da aka kera a Yemen

Saree ya ce an samu nasarar harbo jirgin ne ta hanyar amfani da makami mai linzami na kariyar sama da aka harbawa daga kasa da aka kera a cikin gida.

Har zuwa lokacin fitar da rahoton, rundunar haɗin gwiwar da Saudiya ke jagoranta ba ta fitar da martani kan zargin Houthis ba.

Majiyoyin yankin sun bayyana cewa dakarun Houthi sun harbo jirgin ne kusa da Dutsen Helan, da ke arewa maso yammacin Marib.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Ma'aikata za su huta, dan takara ya yi alkawarin biyan mafi karancin albashin N500,000

Houthis ta ce Saudiya ta kai hare-hare sama da 450

Bayan ikirarin harbo jirgin F-15, Houthi ta ce a wani samame na daban dakarunta sun kuma yi artabu da wasu jiragen yaƙin Saudiya guda biyu da suka je neman tarkacen jirgin da aka harbo.

A cewar Yahya Saree, jiragen yaƙin Saudiya sun kai hare-haren sama sama da 450 tun farkon makon nan.

Ya ce hare-haren sun shafi yankunan Taiz, Lahj, Al-Jawf, Hajjah, Marib, Sa’dah da Al-Bayda.

Saree ya kuma yi ikirarin cewa hare-haren sun haddasa asarar rayuka da jikkata fararen hula, sai dai bai bayyana adadin waɗanda abin ya shafa ba.

Houthis ta yi alkawarin kare sararin samaniyar Yemen

Kakakin sojin ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da take ganin sun dace domin kare ƙasar daga hare-haren waje.

“Za mu ci gaba da kare sararin samaniyar ƙasarmu da ikon mallakarta daga duk wani hari ko take hakki, ta amfani da dukkan hanyoyin da muke da su,” in ji Saree.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hare haren jirage marasa matuka sun jawo gagarumar matsala a Saudiyya

Houthi sun ce suna kare Yemen
Mai magana da yawun rundunar sojojin Houthi, Yahya Saree Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kai hari Mecca

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar tsaron sararin samaniyar Saudiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi mara matuki da kungiyar Houthi ta harba.

Rundunar tsaron ta ce ta harbo jirgin ne kafin ya shiga sararin samaniyar da aka haramta zirga-zirgar jiragen sama a birnin Makka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng