Takarar 2027: INEC Ta Goyi Bayan Tinubu a kan Atiku a Shari'ar da Ake Yi a Kotu
- Hukumar INEC ta nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar Atiku Abubakar kan zargin takardun shaidar karatun Bola Tinubu
- INEC ta ce ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya shigar ba ta da ingantaccen dalili, tana mai cewa Atiku ba shi da haƙƙin shigar da ita
- Hukumar ta kuma ce karɓar takardun da ɗan takara ya gabatar ba ya nufin INEC ta tabbatar da sahihancinsu ko ta yanke hukunci a kansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar kan takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya shigar da ƙarar yana zargin an gabatar da jabun takardu domin cancantar Tinubu ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Source: Facebook
INEC ta yi watsi da ƙarar Atiku
Vanguard ta wallafa cewa INEC ta gabatar da takardar amsa ga kotun ne ta hannun tawagar lauyoyinta karkashin jagorancin Dr Alex Izinyon.
Hukumar ta bayyana ƙarar a matsayin cin zarafin tsarin shari’a, tana mai cewa ba ta bayyana wani ingantaccen dalilin da zai sa kotu ta ci gaba da sauraron ta ba.
Ta kuma ce Atiku ba shi da haƙƙin shigar da ƙarar, domin batutuwan da aka gabatar sun shafi zato ne da kuma muhawarar ilimi kawai.
Maganar takardun Tinubu
Punch ta ruwaito cewa INEC ba ta ce komai kan sahihancin ko rashin sahihancin takardun karatun Tinubu ba.
Sai dai hukumar ta ce ba aikinta ba ne ta zaɓa wa jam’iyya ɗan takara ko ta samar, ƙirƙira ko samo takardun shaidar da ’yan takara suka gabatar.
Ta ce a matsayinta na hukumar da ke gudanar da zaɓe, tana karɓar takardun da ’yan takara suka gabatar ne sannan ta bi ƙa’idojin da Kundin Tsarin Mulkin 1999, Dokar Zaɓe ta 2026 da sauran ƙa’idoji suka tanada.

Source: Facebook
Karin bayani daga INEC
INEC ta ce karɓar wata takarda da ɗan takara ya gabatar ba yana nufin hukumar ta tabbatar da sahihancin duk bayanan da ke cikin takardar ba.
Hukumar ta ce hakan ba hukunci ne na shari’a ko na gudanarwa da ke tabbatar da ingancin takardar ba.
Ta ƙara da cewa Kundin Tsarin Mulki ya riga ya bayyana sharudan cancanta da kuma abubuwan da za su iya hana mutum tsayawa takarar zaɓen gwamnati.
An soki Kwankwaso kan Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa jigon jam’iyyar ADC, Chille Igbawua, ya yi watsi da kiraye-kirayen Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027.
A wata hira da ya yi, Igbawua ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa shekarun Atiku ko lafiyarsa za su hana shi iya jagorantar Najeriya.
Ya ce akwai wasu mutanen da suka fi Atiku ƙuruciya amma ba su da kuzari, basirar tunani da hikimar da yake da su, yana mai cewa shekaru kaɗai ba su isa su tantance ikon mutum na mulki ba.
Asali: Legit.ng

