Majalisar Amurka Ta Ɗauki Gwamna 1 a Najeriya, Ta Karrama Shi da Lambar Yabo Ta Musamman
- Majalisar Wakilai ta Amurka ta karrama Gwamna Hope Uzodimma da lambar yabo saboda kyakkyawan shugabancin da yake yi a Imo
- Wannan karramawa na zuwa ne yayin da Gwamna Uzodinma ke shirin gabatar da jawabi a zauren Majalisar Dattawan Birtaniya
- Majalisar ta yaba da ayyukan da gwamnan Imo ya aiwatar a fannin ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Gabanin jawabin tarihi da zai gabatar a gaban Majalisar Dattawan Birtaniya, gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya samu karramawa ta musamman daga Majalisar Wakilai ta Amurka.
Majalisar wakilan Jihar South Carolina ta Amurka ta karrama Gwamna Uzodinma da lambar yabo saboda irin shugabancin da yake gudanarwa.

Source: Facebook
Vanguard ta ruwaito cewa baya ga jawabin da zai yi a Landan, ana kuma sa ran za a ba Uzodinma lambar yabo ta African Inspirational Leadership and Good Governance.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya
An yaba da manufofin gwamnan Imo
Kafin taron da za a gudanar a Westminster, Majalisar Wakilan Jihar South Carolina ta amince da kudirin yaba wa Uzodimma saboda shugabancinsa karkashin manufofin 3R, wato gyara, sake gina abubuwan more rayuwa da kuma farfado da jihar Imo Wakiliyar majalisar, Rosalyn D. Henderson-Myers, ce ta gabatar da kudirin, wanda ya samu goyin bayan abokan aikinta, kamar yadda The Sun ta rahoto. Majalisar ta yabawa gwamnan kan manyan ayyukan da ya gudanar a fannin hanyoyi, sabunta birane da kuma sauye-sauyen fasahar zamani domin inganta harkokin gwamnati da ci gaba mai dorewa.
Majalisar Amurka ta yabi Uzodinma
A cikin kudirin da Kakakin Majalisar, G. Murrell Smith Jr., da magatakarda, Charles F. Reid, suka sanya wa hannu, an bayyana Uzodimma a matsayin jagora mai kishin ci gaba, wanda ya himmatu wajen shugabanci na bai daya.
Majalisar ta ce hakan ya kara tabbatar da matsayinsa n daya daga cikin fitattun gwamnonin Najeriya masu mayar da hankali kan sauye-sauye da ci gaba.

Kara karanta wannan
Gwamna da wa’adinsa bai kare ba, tsofaffin gwamnoni da masu ci da ke takarar sanata
Majalisar ta ce cikin abubuwan da suka sa aka zabi Uzodimma akwai kokarinsa na inganta yanayin kasuwanci ta hanyar sauye-sauye da manufofin da ke jawo masu zuba jari.

Source: Facebook
Kwamishinan Imo ya karbi lambar yabo
Kwamishinan Yada Labarai, Wayar da Kan Jama'a da Tsare-tsare na Jihar Imo, Hon. Declan Emelumba, ne ya karbi lambar yabon a madadin gwamnan a Landan. Ya bayyana karramawar a matsayin wata shaida ta duniya da ke nuna irin kokarin da Uzodimma ke yi wajen bunkasa Jihar Imo. Emelumba ya yaba wa Majalisar Wakilan Jihar South Carolina bisa wannan girmamawa, yana mai cewa hakan zai kara karfafa wa gwamnan gwiwa wajen ci gaba da yi wa jihar, Najeriya da nahiyar Afirka hidima.
Gwamnan Imo ya yi ƙarin albashi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya sanar da karin mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati daga N76,000 zuwa N104,000.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin gina kyakkyawar alaka da 'yan kwadago, da kuma inganta jin dadin al’ummar jihar baki ɗaya.
Uzodimma ya ce gwamnatin Imo ta dauki matakan karfafa tattalin.arzikin jihar ta hanyar kara kudin shiga daga cikin gida daga N400m zuwa sama da N3bn a kowane wata.
Asali: Legit.ng