INEC Ta Fitar da Sunan Dan Takarar PDP da zai Kara da Bola Tinubu a 2027
- Bangaren jam'iyyar PDP mai goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi murnar fitar da sunan Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa
- Jam'iyyar ta ce matakin da INEC ta ɗauka ya kawo ƙarshen jita-jitar cewa PDP ba za ta iya fitar da ɗan takara ba a zaɓen 2027
- PDP ta kuma yi kira ga mambobin da suka fusata su dawo jam'iyyar domin haɗa kai wajen ƙwato mulki a babban zaɓe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Bangaren jam'iyyar PDP mai biyayya ga Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana farin cikinsa bayan INEC ta fitar da sunan Sanata Sandy Onor a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.
Jam'iyyar ta ce matakin ya kawo ƙarshen watanni na ce-ce-ku-ce da jita-jitar cewa rikicin cikin gida zai hana ta tsayar da 'yan takara a babban zaɓen ƙasa.

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa PDP ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakatarenta na yaɗa labarai na ƙasa, Jungudo Mohammed, ya fitar a ranar Lahadi.
PDP ta yi martani kan matakin INEC
A cewar sanarwar, fitar da sunayen Sanata Sandy Ojang Onor da mataimakinsa, Alhaji Babangida Umar, ya zama babban ci gaba a shirye-shiryen jam'iyyar na tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jam'iyyar ta ce hakan ya tabbatar da cewa duk masu yaɗa jita-jitar cewa ba za ta iya fitar da ɗan takara ba sun yi kuskure.
Ta ce:
"Wannan ci gaban ya kawo ƙarshen yaɗa ƙarya da farfaganda da aka shafe watanni ana yi domin raunana amincewar jama'a da jam'iyyar PDP."
Jam'iyyar ta kuma yaba wa mambobinta da magoya bayanta a Najeriya da ƙasashen waje saboda jajircewarsu duk da ƙalubalen da ta fuskanta.
PDP ta yi kira ga masu fushi su dawo
The Cable ta rahoto cewa PDP ta yabawa INEC, ɓangaren shari'a da hukumomin tsaro bisa abin da ta kira mutunta doka da kundin tsarin mulki.
Haka kuma ta yi kira ga mambobin da suka fusata su dawo cikin jam'iyyar, tana mai cewa haɗin kai ne zai ba ta damar sake karɓar mulki.

Source: Twitter
Jam'iyyar ta ce fitar da sunayen 'yan takararta ya zama babban koma baya ga bangaren da tsohon minista Tanimu Turaki ke jagoranta, wanda ya tsayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takararsa.
INEC ta ƙi karɓar sunan Jonathan
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar INEC ta yi watsi da takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da bangaren PDP na Kabiru Turaki ya miƙa mata.
Bangaren Turaki ya ce ya miƙa sunan Jonathan da sauran 'yan takarorinsa da hannu bayan ya kasa samun lambar shiga tsarin miƙa takardu ta yanar gizo.
Sai dai daraktar wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a ta INEC, Victoria Eta-Messi, ta bayyana cewa hukumar ba ta karɓar sunayen 'yan takara sai ta hanyar tsarin da dokoki suka tanada.
Asali: Legit.ng

