Sama da Mutane 30 Sun Mutu da Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Masu zuwa Jana'iza a Najeriya
- Hukumar SEMA ta jihar Benuwai ta tabbatar da mutuwar fasinjoji sama da 30 a hatsarin jirgin ruwa a mashigar Buruku
- An gano gawarwaki hudu, ciki har da wani limamin Cocin Anglican, yayin da ake ci gaba da neman mutane tara da suka ɓace
- Wasu bayanai sun nuna cewa jirgin ruwan na dauke da fasinjoji sama da 200 lokacin da ya kife a kogin Katsina-Ala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Buruku, Jihar Benue - Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Benuwai (Benue-SEMA) ta tabbatar da mutuwar sama da mutane 30 a hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Asabar da ta wuce.
Jirgin ruwan na gargajiya wadda aka hada da katako ya kife ne yankin mashigar Buruku da ke kogin Katsina-Ala, a Karamar Hukumar Buruku ta jihar Benuwai.

Source: Facebook
Da yake zantawa da Leadership ta wayar tarho ranar Lahadi yayin da yake dawowa daga wurin da hatsarin ya faru, mai magana da yawun Benue-SEMA, Tema Ager, ya ce zuwa yanzu an gano gawarwaki hudu ciki har da wani limamin Cocin Anglican.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Hatsarin jirgi ya rutsa da mutane 70 a hanyar dawowa daga jana'iza
Hukumar SEMA ta ce sama da fasinjoji 200, ciki har da wadanda suka dawo daga gidan ta'aziyya, ne suke cikin jirgin lokacin da ya kife.
An gano gawarwakin mutum 4
A cewar SEMA:
“An tabbatar da mutuwar mutane hudu, yayin da har yanzu mutane tara suka bace. Mun san cewa wadannan mutane tara sun riga sun mutu, amma har yanzu ba a gano gawarwakinsu ba. Don haka, za mu dauke su a matsayin wadanda suka mutu, amma ana neman gawarwakinsu.
“Fasto Moses yana cikin wadanda suka mutu. An ce mutanen da ke cikin jirgin sun haura 200, amma wadanda za a iya tantance adadinsu su ne mutanen da suka je jana’iza, wato masu makoki, saboda wadanda suka dauke su a kan babura za su iya tantance adadinsu.”
SEMA na hasashen rasa rayuka 30
Mai magana da yawun SEMA ya kara da cewa har yanzu ba a tantance wadanda suke bakin kogin da suka raka su wajen tsallakawa zuwa dayan bangaren ba.
Tema Ager ya ce:
"Don haka akwai yiwuwar su ma suna cikin wadanda suka mutu, amma ba a tantance su ba.
"Saboda haka, sama da mutane 30 sun mutu a cikin ruwan. Lokacin da muka je wurin, an fitar da babura biyar daga cikin ruwan, daga cikin babura 38 da suka nutse.”

Source: Original
An dakatar da ayyukan NUMW
Gwamnatin Jihar Benue ta dakatar da ayyukan reshen Kungiyar Ma’aikatan Harkokin Ruwa ta Najeriya (NUMW) na mashigar Buruku nan take sakamakon hatsarin.
Kwamishinan Ruwa da Tattalin Arzikin Shudi, Denis Iyaghigba, ne ya bayar da umarnin bayan ya kai ziyarar tantance halin da ake ciki a wurin hatsarin ranar Asabar, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Yadda kwale-kwale ya kife a Benuwai
Tun farko, kun ji cewa jirgin ruwa dauke da mutane 70 da suka dawo daga jana'iza ya kife yayin tsallake kogin Katsina Ala da ke jihar Benuwai.
Wani ganau a yankin ya ce jirgin ruwan ya yi matukar cika da mutane da kaya fiye da karfinsa lokacin da injinsa ya samu matsala a tsakiyar tafiyar.
Shugaban Karamar Hukumar Buruku, Mista Raymond Zegeya tabbatar da cewa an ceto mutum 60, yana mai cewa ba a san adadin wadanda suka ɓata ba.
Asali: Legit.ng
