'Ba Yan Adawa ba': Atiku Ya Fadi Babban Ƙalubalen Tinubu a Zaɓen 2027
- Atiku Abubakar ya yi magana ga babban abin da zai kawo wa shugaba Bola Tinubu cikas a babban zaɓe mai zuwa
- Atiku da ke takarar kujerar shugaban kasa a ADC ya bukaci shugaban kasa ya mayar da hankali kan tarin matsalolin Najeriya
- Kalaman Atiku sun biyo bayan na ADC da ta zunguri Bola Tinubu game da ikirarin zai yaƙi ƴan adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya zunguro shugaban kasa Bola Tinubu.
A wannan karon ya yi magana game da babbar barazanar da za ta kawo wa Shugaban ƙasa naƙasu a zaɓen da za a yi a 2027.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Atiku na ganin babban kalubalen siyasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fuskanta kafin zaben 2027 ba jam'iyyun adawa ba ne, illa tarihin abin da gwamnatinsa ta gudanar.
Atiku ya soki Tinubu
Jaridar Punch ta wallafa cewa kalaman Atiku na kunshe a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Laraba 29 ga watan Yuli, 2026.
Sanarwar ta ce Atiku ya mayar da martani ne ga kalaman Tinubu cewa shi ba zai ragawa ƴan adawa ba saboda shi a wurinsa ke gezau.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata 28 ga watan Yuli, 2026 a lokacin da ya karbi shugabannin Kungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN).
Shugaban kasar ya tabbatar wa limaman cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta kasance mai zaman kanta, kuma dukkan jam'iyyun siyasa za su samu damar shiga zaben 2027 cikin adalci.
Atiku ya shawarci Tinubu
Da yake martani, Atiku ya zargin Tinubu da fifita nuna karfi a kan ƴan adawa a maimakon mayar da hankali kan shugabanci nagari.
Ya ce abin takaici ne shugaban kasar ya yi irin wannan martani bayan limaman Katolika sun bukaci a gudanar da zabe na gaskiya, adalci da zaman lafiya.

Source: Twitter
A cewarsa, maimakon tabbatar wa 'yan Najeriya cewa zai kare sahihancin zabe, Tinubu ya koma amfani da kalamai masu zafi kan siyasa.
Atiku ya ce kamata ya yi shugaban kasar ya mayar da hankali wajen magance hauhawar farashin kayayyaki, yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin daidaiton canjin kudin naira da kuma raguwar kwarin gwiwar masu zuba jari.
Ya ce:
"Ya kamata shugaban kasa ya fuskanci miliyoyin 'yan Najeriya da ke kwana da yunwa saboda abinci ya zama abin da ba kowa zai iya saya ba."
ADC ta daura kan Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa ADC ta ce ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya mayar da hankali kan yaƙar ƴan ta'adda maimakon adawa gabanin zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani
Jam'iyyar ta ce kalaman Tinubu sun zo ne yayin da rashin tsaro ke ci gaba da ɗaukar rayukan 'yan Najeriya a jihohi da sassaa daban-daban kuma a kullum.
Jam'iyyar adawa a Najeriya ta ce nasarar zaɓe na samuwa ne bisa nagartar aiki, ba barazanar nuna ƙarfin siyasa kamar yadda ake zargin Tinubu ya yi ba.
Asali: Legit.ng
