APC Ta Yi wa Gwamnan Osun Barazana ana Dab da Zabe

APC Ta Yi wa Gwamnan Osun Barazana ana Dab da Zabe

  • Jam'iyyar APC mai mulki ya fara kokarin razana takarar gwamna jihar Osun yayin da ake tunkarar zaben jihar a cikin yan makonni
  • A yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zabe na gwamnan jihar, Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce nasara ta tabbata
  • Manyan da ke cikin kwamitin sun hada da Ibrahim Kabir Masari, sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau da wasu manyan yan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam'iyyar APC ta bayyana cewa babu wani abu da zai hana ta sake karɓe mulkin jihar Osun a zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agustan 2026.

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya bayyana haka a Abuja yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Jam'iyyar na Ƙasa a otal ɗin Transcorp Hilton.

Kara karanta wannan

"Dole mu yi nasara," APC ta dauki babban mataki kan zaben gwamnan jihar Osun

APC ta shaida wa gwamnan Osun ya shirya barin mulki
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe are da 'yan kwamitin yakin neman zaben gwamnan Osun. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Daily Trust ta kawo labarin cewa Yilwatda ya ce jam'iyyar ta tattaro manyan jiga-jigan siyasa domin gudanar da yaƙin neman zaɓe mai ƙarfi da zai kai har matakin unguwanni da gidaje.

APC ta tsokano gwamnan Osun

Trust radio ta ruwaito cewa ya kuma tabbatar wa magoya bayan APC cewa za su yi gangamin neman ƙuri'u daga gida zuwa gida domin sake kwato gidan gwamnatin jihar Osun.

A cewarsa, yawan gwamnoni, 'yan majalisa da kuma waɗanda suka sauya sheƙa daga jam'iyyun adawa zuwa APC zai ƙara wa jam'iyyar ƙarfi.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne shugaban Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, ya ce za su gudanar da kamfen cikin tsari, lumana da kuma mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi al'umma.

Ya ce kwamitin zai bayyana nasarorin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ƙarfafa tuntuɓar masu kaɗa ƙuri'a a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

APC ta godewa Tinubu

A ɗaya hannun kuma, ɗan takarar gwamnan APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji (AMBO), ya gode wa Shugaba Tinubu da shugabannin jam'iyyar bisa goyon bayan da suke ba shi.

Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa sun shirya karbe gwamnatin jiha
Nentawe Yilwatda da wasu manyan APC Hoto: Professor Nentawr Yilwatda
Source: Facebook

Uzodimma ya ce:

"Yaƙin neman zaɓenmu ba tare da tashin hankali ba, mai gogayya ba tare da ƙiyayya ba, kuma cike da ƙwarin gwiwa ba tare da girman kai ba."

An kuma bayyana cewa Gwamna Uzodimma ne ke jagorantar kwamitin yaƙin neman zaɓen, yayin da Ibrahim Kabir Masari ke mataimakin shugaba, sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, wanda ke matsayin sakatare, tare da wasu gwamnoni, ministoci da 'yan majalisar tarayya.

An kai wa jigon APC hari

A baya, mun kawo labarin cewa wasu mahara da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun harbi wani ’dan jam'iyyar APC, Taofeek Mustapha a jihar Osun yayin da babban zaben jihar ke kara karatowa.

Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da samun rigingimun siyasa gabanin zaben gwamnam jihar Osun da za a yi a watan Agusta, 2026 yayin da siyasa ke kara daukar zafi

Jigon jam'iyyar APC da aka harba da bindiga, Taofeek Mustapha ya ce yana sanye da hular kamfen mai tambarin AMBO lokacin da aka kawo harin, lamarin da ya sa aka rika jefa zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng