'Yan Sanda Sun Cafke Matasa kan Sanya Rigar 'Tinubu Must Go'
- Rundunar ’yan sandan Borno ta kama mutane biyar tare da gurfanar da su bisa zargin buga wa da sanya riga mai ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”
- Mutanen sun musanta aikata laifuffukan da ake zarginsu da su, yayin da kotu ta ɗage sauraron batun belinsu zuwa ranar 6 ga Oktoba 2026
- Amnesty International ta soki tuhumar, tana mai cewa bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana ta hanyar sanya tufafi na cikin ’yancin ɗan Adam
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - 'Yan sanda a Borno sun kama tare da gurfanar da wasu matasa biyar a Maiduguri bisa zargin buga wa da sanya riga mai ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”, wato “Tinubu ya tafi”.
Mutanen da ake zargin sun hada da Baba Aji Gremami mai shekaru 44, Mustapha Abba Yemen mai shekaru 28, Abbacha Mohammed Ali mai shekaru 32, Adam Umar Gubio mai shekaru 21 da Abdulhamid Mohammed mai shekaru 21.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce rahoton farko na laifi (FIR) da Sashen Binciken Manyan Laifufduka na Jihar (SCID) ya fitar, kuma jami’an kotu suka tabbatar, lamarin ya faru ne ranar 25 ga Satumba 2026.
An kama su a Maiduguri
Takardar, wadda aka sanya wa ranar 29 ga Satumba 2026, ta ce an kama mutanen ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a yankin West End Roundabout da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
’Yan sandan sun tuhume su da laifuffukan haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da zaune tsaye, haddasa rikicin zaman lafiya da kuma daba.
Masu gabatar da ƙara sun ce waɗannan laifuffuka sun saba da tanade-tanaden Sashe na 60, 78, 79 da 392 na Kundin Dokokin Laifuka na Jihar Borno.
Mutanen sun musanta aikata laifin
Lokacin da aka gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Majistare ta ɗaya da ke Maiduguri, dukkan mutanen biyar sun musanta aikata laifuffukan da ake tuhumarsu da su.
Lauyoyinsu sun kuma gabatar da bukatar a ba su belinsu domin su kasance a waje yayin da ake ci gaba da shari’ar.
Alƙalin da ke jagorantar shari’ar ya ɗage yanke hukunci kan bukatar belin zuwa ranar 6 ga Oktoba 2026. A gefe guda, an sanya ranar 26 ga Oktoba 2026 domin fara sauraron cikakkiyar shari’ar.
Amnesty ta soki kamen
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International (AI) ta yi kakkausar suka kan tuhumar da aka yi wa mutanen biyar.
Ƙungiyar a wani rubutu a shafinta na Facebook ta bayyana tuhumar a matsayin abin mamaki, tare da cewa tsare mutanen ya kasance wani nau'i na kamen ba bisa ƙa’ida ba.
Amnesty International ta jaddada cewa bayyana ra’ayin siyasa cikin lumana, ciki har da amfani da tufafi wajen nuna rashin amincewa da gwamnati, wani muhimmin ɓangare ne na ’yancin ɗan Adam, ba laifi ba.

Source: Facebook
Batun rashin lafiyar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan batun lafiyarsa da ake ta yayatawa.
Shugaba Tinubu ya yi watsi da damuwar da wasu ke nunawa game da lafiyarsa, yana mai cewa yana cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki bayan dawowarsa Najeriya daga Turai.
Asali: Legit.ng
