Gwamnonin APC Sun Dauki Matsaya bayan Nazari kan Waɗanda Suka Samu Tikitin Takara a 2027
- Gwamnonin jam'iyyar APC sun zauna sun yi nazari kan zabukatar fitar da 'yan takara da jam'iyya mai mulki ta gudanar a makonnin da suka shige
- Bayan kammala nazari kan sakamakon zabukan, gwamnonin sun yanke shawarar ganawa da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentwe Yilwatda
- Sun kuma kuduri aniyar hada kai domin magance matsalolin da ke fuskantar ƙasa da kuma tabbatar da cewa rayuwar ’yan Najeriya ta inganta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnonin jihohin da aka zaba a karkashin APC sun sake duba sakamakon zabukan fitar da gwani na jam’iyyar, wanda aka gudanar a kwanakin baya.
Gwamnonin sun yanke shawarar ganawa da shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da sauran shugabannin APC gabanin zaben 2027.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce shugaban kungiyar gwamnonin APC (PGF) kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana hakan bayan taron da suka gudanaf a Abuja, wanda ya kare da sanyin safiyar Talata.

Kara karanta wannan
2027: An miƙa bukata ga Kwankwaso da Obi bayan an fara jita jitar za su fice daga NDC
Sun yabawa sakamakon zabukan APC
Uzodimma ya ce gwamnonin sun sake nazarin yadda zabukan fitr da gwani na jam’iyyar suka gudana a fadin kasa, tare da duba sakamakon zaben gwamnan Jihar Ekiti da kuma zabukan cike gurbi da aka gudanar
A cewarsa, gwamnonin sun kuma kuduri aniyar hada kai domin magance matsalolin da ke fuskantar tsarin dimokuradiyya da kuma tabbatar da cewa rayuwar ’yan Najeriya ta inganta.
Gwamna Uzodinma ya ce:
“Mun kuduri aniyar yin aiki tare domin magance matsaloli da kalubalen da ke gaban dimokuradiyyarmu, tare da tabbatar da cewa al’ummarmu sun fi samun walwala.”
APC ta fara shirye-shiryen zaben 2027
Uzodimma ya kara da cewa gwamnonin sun amince da shirya ganawa da shugabannin jam’iyyar domin tsara dabarun tunkarar zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki na shekarar 2027.
Ya bayyana cewa APC ta fara shirye-shiryen zaben kuma tana da kwarin gwiwar samun nasara, cewar rahoton Bussiness Day.
“Mun amince za mu je mu gana da shugabannin jam’iyyar APC domin tsara yadda za mu tunkari zabukan shugaban kasa da na Majalisar Dokoki na 2027. Mun shirya tsaf kuma muna da yakinin samun nasara.”

Source: Twitter
Gwamnonin sun jaddada mubaya'a ga APC
Shugaban PGF ya ce kungiyar gwamnonin ta sake tabbatar da aniyarta ta ci gaba da aiki tare da shugabancin APC domin kara karfafa jam’iyyar da kuma shirya ta yadda ya kamata domin zabukan da ke tafe.
Taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Ekiti, Zamfara, Taraba, Legas, Sokoto, Kano, Kaduna, Gombe, Kebbi, Akwa Ibom da Borno, tare da sauran gwamnonin jam'iyyar APC.
APC ta yi murna da nasarar gwamnan Ekiti
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta aika da sakon taya murna ga zaɓabɓen gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.
Jam'iyyar APC ta taya Biodun Oyebanji murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Ekiti na ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.
T bayyana cewa nasarar Vwamna Biodun Oyebanji a zaben da ya gabata cike take da tarihi, domin ya zama gwamnan farko da ya yi tazarce a jihar Ekiti.
Asali: Legit.ng
