Abin da Abdulsalami Ya Fadawa Shugaban INEC game da APC, PDP, ADC gabanin 2027

Abin da Abdulsalami Ya Fadawa Shugaban INEC game da APC, PDP, ADC gabanin 2027

  • Abdulsalami Abubakar ya buƙaci hukumar INEC ta gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da rashin nuna son kai
  • Ya gargadi shugaban hukumasr INEC da kada ya bari matsin lambar 'yan siyasa ya karkatar da shi daga rantsuwar aikinsa
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar da cewa ƙuri'un 'yan Najeriya za su ƙidayu a zaɓen Osun da babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Neja - Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya buƙaci hukumar INEC da ta kasance mai gaskiya da adalci wajen gudanar da ayyukanta, tare da kauce wa duk wani matsin lambar siyasa kafin zaɓen gwamnan Osun da babban zaɓen shekarar 2027.

Abdulsalami, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa, ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a lokacin da shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), tare da kwamishinonin hukumar suka kai masa ziyarar girmamawa a gidansa da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Abdulsalami Abubakar ya bukaci shugaban INEC ya yi wa jam'iyyu adalci gabanin 2027
Shugaban hukumar INEC ya na musabaha da Abdulsalami Abubakar a gidansa da ke Minna, jihar Neja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Abdulsalami ya ba shugaban INEC shawarwari

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tawagar shugabannin INEC ta kuma kai irin wannan ziyara ga tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, a gidansa da ke Minna.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Abdulsalami ya ce aikin shugaban INEC na daga cikin manyan mukamai masu muhimmanci a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya, saboda yadda duk wani zaɓe ke da tasiri kai tsaye kan makomar ƙasa.

Ya bayyana cewa duk wani shugaban INEC kan fuskanci suka daga jam'iyyun siyasa, musamman idan sakamakon zaɓe bai yi wa wasu daɗi ba.

A cewarsa, duk jam'iyyar da ta sha kaye za ta nemi wani dalili na zargin hukumar da nuna son kai.

Abdulsalami ya gargadi shugaban INEC

Abdulsalami ya ci gaba da cewa:

"Mukaminka yana da matuƙar muhimmanci ga dimokuraɗiyyarmu. Dole ne ka yi aiki tukuru domin ka samu amincewar 'yan siyasa, saboda duk abin da kai da kwamishinoninka kuka yi, za a zarge ku da nuna son kai ta wata hanya ko wata."

Kara karanta wannan

"Da an kai shi gidan yari"; Fadar shugaban kasa ta jikawa Atiku aiki kan taba Tinubu

Ya ƙara da cewa:

"Idan wata jam'iyya ta faɗi zaɓe, kai ne za ka zama abin zargi. Za su nemi hujjoji su ce INEC ta yi kuskure. Amma da amincewar da muke da ita a gare ka, ina da tabbacin za ka yi iya ƙoƙarinka domin amfanin ƙasar nan."

Ya ƙara da cewa makomar dimokuraɗiyyar Najeriya na hannun INEC da shugabanninta, saboda haka ya yi addu'ar Allah ya ba su hikima da ƙarfin guiwar gudanar da aikinsu cikin gaskiya.

Shugaban INEC ya ba Abdulsalami Abubakar tabbacin yin adalci a zaben 2027
Abdulsalami Abubakar ya karbi bakuncin shugaba da kwamishinonin INEC a gidansa na Minna, jihar Neja. Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Shugaban INEC ya ba da tabbaci kan 2027

A nasa jawabin, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ƙuri'unsu za su ƙidayu a zaɓen gwamnan Osun da kuma babban zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce girmama tsoffin shugabannin ƙasar saboda irin gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya, dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa, tare da neman shawarwari da addu'o'insu domin samun nasarar gudanar da zaɓukan da ke tafe.

Kara karanta wannan

APM ta fadi abin da ya firgita Bola Tinubu game da zaben 2027

Duba hotunan ziyarar da aka wallafa a shafin INEC na X a kasa:

Abdulsalami ya hana Obasanjo zuwa kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana yadda ya shawarci Olusegun Obasanjo game da tsayawa takara a zaben 1999 .T

sohon shugaban mulkin sojan ya ce gwamnatinsa ba ta goyi bayan Obasanjo ba, duk da rade-radin cewa sun taimaka masa ya zama shugaban kasa.

Abdulsalami ya bayyana cewa ya sassauta ka'idojin rajistar jam'iyyu domin AD ta samu shiga, ta tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com