Mara Lafiya Ya Mutu bayan Tare Motar Asibiti don Motocin Babban Minista Su Wuce

Mara Lafiya Ya Mutu bayan Tare Motar Asibiti don Motocin Babban Minista Su Wuce

  • Rasuraj Chakraborty ya rasu a asibiti bayan an dakatar da motar asibitin da ke ɗauke da shi domin ayarin shugaban gwamnatin Assam ya wuce
  • Bidiyon lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a Assam, inda aka dakatar da jami’an ’yan sanda huɗu da ake dangantawa da dakatar da motar
  • Babban Minista, Himanta Biswa Sarma ya ba da haƙuri, yana mai cewa bai kamata a hana motar asibiti ko wata motar gaggawa wucewa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Assam, India - Rasuraj Chakraborty, wani mara lafiya da ke fama da matsananciyar rashin lafiya a India, ya rasu bayan ’yan sanda sun dakatar da motar asibitin da ke ɗauke da shi domin ayarin Babban Minista na Assam, Himanta Biswa Sarma, ya wuce.

An tabbatar da rasuwar a asibitin Chakraborty a Silchar Medical College and Hospital ranar 1 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi maganar hana hawa a Kano bayan kalaman bangaren Aminu Ado

Mara lafiya ya mutu a India
'Yan sanda sun tare wasu masu ababen hawa a India Hoto: Leon Neal
Source: Getty Images

Rahoton jaridar India Today ya ce Chakraborty, mazaunin Bangar da ke gundumar Sribhumi, yana fama da cutar da ta shafi hanta.

An kawo shi daga Sribhumi zuwa Silchar Medical College and Hospital ranar Laraba domin samun ƙarin kulawa ta musamman bayan rahotanni sun ce yanayinsa ya tsananta.

An dakatar da motar asibitin

A cewar rahotanni, ’yan sandan da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a yankin Ramnagar ISBT da ke Silchar ne suka dakatar da motar asibitin 108 domin ba ayarin shugaban gwamnatin Assam damar wucewa.

Bidiyon lamarin da aka wallafa a kafafen sada zumunta ya jawo fushin jama’a da ce-ce-ku-ce a faɗin Assam.

Bayan faruwar lamarin, an dakatar da jami’an ’yan sanda huɗu da ake dangantawa da abin da ya faru.

Babban Minista ya yi magana

Sai dai Sarma ya bayyana a ranar Alhamis cewa dakatar da motar asibitin na ɗan lokaci domin ayarinsa ya wuce ba shi da alaƙa da rasuwar Chakraborty.

Kara karanta wannan

Najeriya ta ƙulla alaƙa da sojojin Amurka yayin da ta'addanci ya yi ƙamari

Ya ce marigayin na fama da matsananciyar cutar hanta, kuma rasuwarsa ba ta da alaƙa da ɗan dakatarwar da aka yi wa motar asibitin na wasu daƙiƙu.

Sarma ya kuma ce bai kamata a jefa jama’a cikin wahala saboda zirga-zirgar ayarinsa ko na wani minista ba, jaridar

Ya ce shi kansa ba ya son yin zirga-zirga da ayari, amma kwamishinonin gundumomi da jami’an ’yan sanda ne ke shirya masa hakan.

Babban Minista ya ba da haƙuri

Duk da bayanin da ya yi, Sarma ya ba da haƙuri ga jama’a, yana mai cewa bai kamata a dakatar da motar asibiti, motocin kashe gobara ko wasu motocin gaggawa saboda ayarin manyan jami’an gwamnati ba.

“Babban Minista bawan jama’a ne kawai, kuma a sabuwar Assam babu gurbin al’adar fifita manyan mutane.” In ji shi.

An ba jami'an tsaro umarni

Tun da farko ranar Alhamis, Ofishin Babban Minista na Assam ya bayar da umarni ga dukkan kwamishinonin gundumomi da manyan jami’an ’yan sanda da su tabbatar da cewa zirga-zirgar ayarin shugaban gwamnatin ba ta haifar wa jama’a da wata matsala ba.

Kara karanta wannan

Masifa ta auka wa masu hakar ma'adanai a Bauchi, an rasa rayuka

Mara lafiya ya gamu da ajalinsa a India
Masu ababen hawa na jira bayan 'yan sanda sun tare hanya a India Hoto: Leon Neal
Source: Getty Images

Umarnin ya ce an riga an bai wa dukkan DCs da SSPs cikakken umarni cewa ba za a hana motocin asibiti, motocin kashe gobara da sauran motocin gaggawa wucewa ba yayin da ayarin manyan jami’an gwamnati ke tafiya.

Umarnin ya sake jaddada cewa a kowane hali bai kamata shirye-shiryen ayarin manyan jami’an gwamnati su zama dalilin hana motocin asibiti ko wasu motocin gaggawa wucewa ba.

Hamshakin attajiri ya mutu

A wani labarin kuma kun ji cewa attajirin Zimbabwe kuma ɗan kasuwa, Wicknell Chivayo, da matarsa Lucy Muteke, sun mutu.

Hamshakin dan kasuwar da matarsa sun mutu ne a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu da ya yi sanadin mutuwar mutane shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng