Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Saki Sunayen Mutane 5 da take Nema Ruwa a Jallo

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Saki Sunayen Mutane 5 da take Nema Ruwa a Jallo

  • 'Yan sandan Osun sun ayyana mutum biyar da ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a rikicin siyasar da ya yi sanadin rasa rayuka
  • 'Yan sanda sun bukaci al'umma su taimaka da bayanan da za su kai ga cafke mutanen, tare da tabbatar da kudirinsu na wanzar da zaman lafiya
  • A gefe guda, 'yan takarar jam'iyyar AP sun zargi rundunar da kama mambobinsu bisa dalilan siyasa, tare da neman daukin gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Osun – Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta ayyana wasu mutane biyar da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu a tashe-tashen hankula da suka biyo bayan rikicin siyasa da ya addabi jihar cikin 'yan watannin nan.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abiodun Ojelabi, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce jami'an tsaro na kara kaimi wajen cafke duk wadanda ake zargi da hannu a kashe-kashe da lalata dukiyoyi da suka faru sakamakon rikicin.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin jami'an tsaro da ƴan bindiga a Katsina, an rasa rayuka

'Yan sanda sun ayyana neman wasu mutane 5 kan haddasa rikici a Osun
Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan sanda na neman mutane 5

Mutanen da rundunar ta ayyana ana nema sun hada da Dauda Olamilekan wanda aka fi sani da Emir, Taoreed wanda ake wa lakabi da Small Rugged, Adetunji Kamoru Olatunde, Saka Afees wanda aka fi sani da Terror, da kuma Adeyemi Saheed, in ji rahoton Vanguard.

Rundunar ta bukaci duk wanda ke da wani sahihin bayani game da inda ake zargin mutanen suke da ya sanar da ofishin 'yan sanda mafi kusa domin daukar matakin da ya dace.

Haka kuma ta roki mazauna jihar su ci gaba da kai rahoton duk wani abin da ya shafi aikata laifuka domin taimakawa kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Rikicin siyasa ya yi sanadin rasa rayuka

Tun daga watan Yuni ne rikicin siyasa ya kara kamari a sassa daban-daban na jihar Osun, inda aka samu kashe-kashe da dama.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai wani matashi mai suna Olapade Ezekiel a Ilobu, Comrade Abdullateef Olamilekan, Kazeem Akande mai shekaru 70 a Osogbo, Ajayi Aderogba a Esa-Oke, da wani mutum mai suna Eluyera a Ikire.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da daukar matakan tabbatar da zaman lafiya tare da gurfanar da duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a aikata laifuka.

Kofarin jam'iyyar AP kan 'yan sanda

Jam'iyyar Accord ta zargi 'yan sanda da kama wasu mambobinsu
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke da tutar jam'iyyarsa ta Accord. Hoto: @AAdeleke_01
Source: Twitter

A wani bangare kuma, 'yan takarar jam'iyyar Accord sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, DIG Tunji Disu, Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Hukumar Kare Hakkin Dan Adam (NHRC) da sauran masu ruwa da tsaki su kawo musu dauki.

Jaridar The Guardian ta rahoto cewa sun zargi rundunar 'yan sandan Osun da aiwatar da kama da tsare wasu jagororinsu bisa dalilan siyasa da kuma amfani da korafe-korafen da suka kira na bogi wajen gallaza musu.

Mai magana da yawun 'yan takarar jam'iyyar Accord na majalisun dokoki, Bamidele Salam, ya bayyana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Osogbo cewa rundunar 'yan sanda na bai wa wasu 'yan siyasa damar amfani da ita wajen cimma manufofinsu.

Jam'iyyar Accord ta nuna goyon baya ga Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Ademola Adeleke da shugabannin jam’iyyar Accord na ƙasa sun amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a 2027.

Kara karanta wannan

An ayyana neman wani sojan Najeriya ruwa a jallo, an saki hotuna da bayanansa

Shugabannin jam’iyyar sun ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta kammala manyan ayyukan tituna da ababen more rayuwa da ta fara.

Gwamnan na jihar Osun da shugabannin sun kuma yi gargaɗi kan tashin hankali, tsoratarwa da magudin zaɓe a zaɓen gwamnan Osun na watan Agustan shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com