An Saki Hoton Gurgu da Bingigogi da ke Taimakon 'Yan Bindiga
- Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kwara sun kama wani matashi gurgu mai shekaru 30 bisa zargin safarar makamai
- 'Yan sanda sun sami nasarar kwato bindiga nau'in AK-47 guda biyu da kuma harsashi guda 42 daga hannun wanda ake zargin
- Kama shi ya biyo bayan gudanar da bincike na kwatsam da jami'ai suka gudanar a kan hanyar Alapa zuwa Okolowo a birnin Ilorin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ilorin – Rahoto ya nuna cewa rundunar 'yan sandan jihar Kwara ta sanar da kama wani mutum da ake zargi da hannu a harkar safarar makamai a jihar.
Wanda ake zargin, wani matashi mai suna Umaru mai shekaru 30, jami'an 'yan sanda sun damke shi shi ne a cikin wata motar kasuwa a lokacin da suke gudanar da bincike a kan hanyar Alapa zuwa Okolowo a birnin Ilorin.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta rahoto cewa jami'an tsaro sun sami nasarar gano bindigu nau'in AK-47 guda biyu masu aiki da kuma harsasai masu guda 42 a cikin wata jakar da ke cikin motar.
Yadda aka gano wanda ake zargin
Mataimakiyar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Ta bayyana cewa da farko Umaru ya musanta mallakar jakar da aka gano makaman a ciki, sai dai bayan zurfafa bincike, daga karshe ya amsa laifinsa na kasancewa mai jigilar makaman.
A cewar PPRO na jihar Kwara:
"Wanda ake zargin ya bayyana cewa wani mamban hanyar safarar makamai mai suna Dan Yarubawa ne ya mika masa makaman domin ya kai wa wani mutum mai suna Dahiru a wajen jihar Kwara."
Bayanin kwamishinan 'yan sanda
Kwmishinan 'yan sandan jihar Kwara, CP Ojo Adekimi, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar tana nan tsaye tsayin daka wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Ya bukaci al'umma da su ci gaba da ba jami'an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da muhimman bayanai domin dakile ayyukan bata-gari a faɗin jihar.

Source: Original
A halin yanzu, rundunar 'yan sanda ta tsananta bincike domin kama sauran mutanen da ke da alaƙa da wannan tsarin safarar makamai.
Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa hoton wanda ake zargin dauke da bindigogi biyu a tare da shi a shafinsa na X.
An kashe shugaban ISWAP
A wani labarin, mun ruwaito cewa haɗin gwiwar jami'an tsaro sun sami nasarar kashe wani babban shugaban kungiyar ISWAP mai suna Abdussamad Ohida a dajin Owo da ke jihar Ondo.
Samamen na musamman wanda aka gudanar a ƙarshen mako, ya samu halartar jami'an tsaron farin kaya na DSS, sojojin Najeriya, da kuma jami'an tsaro na Amotekun.
An kashe Ohida, wanda aka fi sani da Anwar, tare da sauran mambobin kungiyar a lokacin da yake shirin kaddamar da muhimman hare-hare a jihohin Kudancin kasar nan.
Asali: Legit.ng

