Yan Sandan MOPOL Sun Nemi Agajin Sufeton Ƴan sanda Watanni 7 da Hana Su Alawus
- Yan sandan MOPOL da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar Filato sun ce ba a biya su alawus na watanni bakwai ba
- Jami'an bayyana wadanda su ke zargi a cikin 'yan sanda da karkatar da kudin alawus da gwamnatin Filato ke fitarwa
- Sun roki Sufeto Janar na 'Yan Sanda da ya binciki lamarin tare da tabbatar da an biya su hakkokinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Wasu jami'an Rundunar 'Yan Sandan MOPOL da aka tura aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato sun zargi wasu manyan jami'an rundunar da karkatar da kudin alawus da gwamnatin jihar ke ware masu.
Daya daga cikin jami'an, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce an turo su daga jihar Kano zuwa kauyukan da ke kananan hukumomin Jos ta Kudu, Barkin Ladi, Bokkos da wasu yankuna domin taimakawa wajen dakile hare-hare da kashe-kashe.

Source: Twitter
Rahoton Daily Trust ta ruwaito jami'in ya ce an tura su aikin ne tun watan Disamban 2025, amma ba sa karbar alawus na wata-wata na N150,000 da aka yi masu alkawari.
Yan sanda sun nemi ɗauki a Filato
Rahoton ya ce a cewarsa, ranar da suka isa Filato an kai su Gidan Gwamnati da ke Jos, inda aka yi masu alkawarin za a rika biyansu alawus na wata-wata.
Ya kara da cewa bayan sun karbi na watan Disamba, ba su sake samun komai daga watan Janairu zuwa Yuli 2026 ba, duk da cewa sun samu bayanin cewa gwamnatin jihar tana sakin kudin kowane wata.
Ya ce:
"Gwamnatin jihar ta yi mana alkawarin biyan alawus. Mun samu sahihin bayani cewa ana fitar da kudin kowane wata, amma ba ya zuwa hannunmu. Wannan shi ne wata na bakwai ba tare da an biya mu komai ba. Ba mu san wanda ke karkatar da kudin ba."
Kiran yan sanda ga IGP
Wani jami'in da abin ya shafa ya shaida cewa an tura su wurare masu nisa, kuma albashinsu kadai bai isa ya ciyar da su a wurin aiki tare da tallafa wa iyalansu ba.
Ya ce suna dogaro da alawus din ne domin kara wa kudin shigarsu karfi da kuma gudanar da rayuwa da ta iyalansu.
Ya kara da cewa saboda tsadar rayuwa da ake fama da ita, wasu daga cikinsu sun kasa biyan kudin hayar gidajensu, har ma wasu masu gida sun ba su sanarwar ficewa.

Source: Original
Wani jami'in kuma ya ce dokokin MOPOL sun tanadi cewa duk jami'in da aka tura aiki na musamman daga jiharsa zuwa wata jiha ya cancanci alawus, amma a nasu yanayin ana karkatar da kudin. Ya ce wasu rukunan jami'an da aka turo bayansu sun karbi nasu alawus, amma su ba su samu komai ba kuma sun bi hanyoyi daban-daban wajen neman hakkokinsu amma har yanzu ba a dauki wani mataki ba.
A cewarsa:
"Rike mana wannan kudi take hakkinmu ne. Wannan hakki ne da doka ta tanadar mana, ana sakin kudin amma wasu tsirarun mutane suna karkatar da shi."
Sun yi kira ga Sufeto Janar na 'Yan Sanda da sauran masu ruwa da tsaki da su binciki lamarin tare da tabbatar da an biya su dukkan hakkokinsu.
Yan sanda sun yi fallasa
A baya, mun kawo labarin cewa yan sandan Osun sun ayyana mutum biyar da ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a rikicin siyasar da ya yi sanadin rasa rayuka.
Rundunar 'yan sanda ta bukaci al'umma su taimaka da bayanan da za su kai ga cafke mutanen, tare da tabbatar da kudirinsu na wanzar da zaman lafiya.
A gefe guda, 'yan takarar jam'iyyar AP sun zargi rundunar da kama mambobinsu bisa dalilan siyasa, tare da neman daukin gwamnatin tarayya a cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng


