Kotun Daukaka Kara Ta Jingine Hukunci a Shari'ar Soke Rajistar ADC da Jam'iyyu 4
- Kotun Daukaka Kara ta saurari daukaka karar ADC da wasu jam'iyyu hudu, sannan ta jingine hukunci kan bukatar soke umarnin kotun tarayya
- A baya kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncin soke rajistar jam'iyyun, tare da caccakar alkalin kotun tarayya saboda saba umarninta
- Hukuncin da Kotun Daukaka Kara za ta yanke zai iya shafar makomar ADC da sauran jam'iyyu kafin babban zaben shekarar 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta saurari karar daukaka kara da aka shigar domin soke hukuncin da ya umarci hukumar INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam'iyyun siyasa hudu.
Kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari'a Abba Mohammed ya jingine ranar yanke hukunci bayan dukkan bangarorin da ke karar sun amince da hujjojinsu a gaban kotun.

Source: Twitter
Jam'iyyu 5 sun kalubalanci hukuncin kotu
Baya ga ADC, sauran jam'iyyun da suka nemi a soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya sun hada da APP, AA, AP da ZLP kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ya nuna.
A ranar 16 ga watan Yuni, Kotun Daukaka Kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, tare da caccakar Mai Shari'a Peter Lifu bisa ci gaba da sauraron shari'ar duk da umarnin da kotun daukaka kara ta bayar.
Kotun ta bayyana cewa tun a ranar 22 ga watan Mayu ta umurci alkalin da ya dakatar da shari'ar har sai an kammala sauraron karar daukaka kara, amma ya yi watsi da umarnin tare da ci gaba da yanke hukunci.
Kotun daukaka kara ta caccaki alkali
Kotun Daukaka Kara ta bayyana matakin alkalin a matsayin rashin mutunta tsarin shari'a, tana mai cewa Kotun Koli ta taba bayyana irin wannan hali a matsayin abin da bai dace da alkali ba.

Kara karanta wannan
Matsala ta tunkaro ADC da kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben shugabanni
A hukuncinsa, Mai Shari'a Peter Lifu ya umurci INEC ta soke rajistar jam'iyyun biyar saboda, a cewarsa, sun kasa cika sharudan kundin tsarin mulki da ke ba su damar ci gaba da kasancewa a matsayin halastattun jam'iyyun siyasa.

Source: UGC
Hukuncin kotun ya shafi zaben 2027
Kotun Tarayya ta kuma haramta wa INEC ci gaba da amincewa da jam'iyyun, karbar sunayen 'yan takararsu ko ba su damar shiga babban zaben shekarar 2027.
Alkalin ya kuma umurci jam'iyyun su daina bayyana kansu a matsayin halastattun jam'iyyun siyasa, bayan ya yanke cewa karar da kungiyar National Forum of Former Legislators (NFFL) ta shigar tana da inganci.
Kungiyar NFFL ta bukaci kotun ta fayyace ko kundin tsarin mulki ya wajabta wa INEC soke rajistar jam'iyyun da suka kasa cika sharudan da ke karkashin sashe na 225A na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, tare da tanadin Dokar Zabe da ka'idojin INEC.
An dakatar da soke rajistar ADC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci INEC ta soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu.
Alkalan kotun sun umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta jira a kammala sauraron karar da ke gabanta kafin daukar wani mataki kan jam’iyyun.
Kotun Daukaka Karar ta soki hukuncin da kotun tarayya ta yanke, tana mai bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa tsarin shari’ar Najeriya.
Asali: Legit.ng

