APM Ta Fadi Abin da Ya Firgita Bola Tinubu game da Zaben 2027
- Jam'iyyar APM ta ce kalaman gwamnatin Bola Tinubu kan Gwamna Seyi Makinde sun nuna shugaban ƙasa na cikin fargaba kan zaben 2027
- Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa Makinde zai kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa saboda irin goyon bayan da yake samu daga 'yan Najeriya
- APM ta ce ba za ta yi zage-zage ba, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi rayuwar al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam'iyyar APM ta yi ikirarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na cikin fargaba sakamakon yadda ɗan takararta na shugaban ƙasa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ke ƙara samun karɓuwa a gabanin zaben 2027.
Jam'iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Abubakar Yusuf, ya fitar ranar Laraba.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta zo ne bayan mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana a wata hira cewa Makinde da jam'iyyar APM ba su da wani tasiri a siyasar zaben 2027.
APM ta yi wa Bwala martani
Da take mayar da martani, APM ta ce abin takaici ne yadda gwamnatin Tinubu ke amfani da kalaman cin mutunci maimakon mayar da hankali kan matsalolin da suka addabi 'yan Najeriya.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin ba ta da gamsasshen tarihin ayyukan da za ta gabatar wa jama'a, saboda haka take komawa ga abubuwa marasa inganci.
Sanarwar ta ce:
"Abin takaici ne cewa gwamnatin Tinubu ta kai matsayin da take dogaro da mutane wajen suka kan masu adawa maimakon magance matsalolin da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya."
APM ta kuma yi ikirarin cewa kalaman Daniel Bwala za su dawo su ci shi a gaba yayin da siyasar 2027 ke ƙara karatowa.
An yi hasashen nasarar Makinde
Jam'iyyar APM ta ce zaben shugaban ƙasa na 2027 zai kasance tsakanin Gwamna Seyi Makinde da Shugaba Bola Tinubu.
Ta yi zargin cewa miliyoyin 'yan Najeriya sun yanke shawarar sauya gwamnati saboda matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ake fuskanta.
A cewar jam'iyyar, Makinde zai shiga zaben ne da abin da ta kira kyakkyawan tarihin gudanar da mulki a jihar Oyo, inda ta ce ya kawo ci gaba a fannoni daban-daban.
Har ila yau, APM ta yi ikirarin cewa sama da matasa miliyan 50 suna goyon bayan Makinde kuma suna shirye su zaɓe shi a zaben 2027.

Source: Facebook
APM ba za ta yi zagi ba
Rahoton da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa jam'iyyar ta jaddada cewa ba za ta shiga musayar zagi da gwamnatin tarayya ba.
A maimakon haka, ta ce za ta ci gaba da gabatar da manufofinta kan farfaɗo da tattalin arziki, inganta tsaro, samar da ayyukan yi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma sake gina ababen more rayuwa.
Ana so Tinubu ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya hakuri tare da yin murabus kan ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye hukumar PFIPC.
Atiku ya ce saɓanin bayanan da Akanta Janar na Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) suka bayar kan buɗe asusun bankin PFIPC ya tayar da tambayoyi masu yawa game da yadda aka tafiyar da lamarin.
Ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar abin da ya faru, ko kuma ya ɗauki alhakin abin da ya kira rikicin bayanan hukumomin gwamnati.
Asali: Legit.ng


