Fargabar Juyin Mulki: Yadda Tinubu Ya dage Faretin Sojoji Shekaru 2 a Jere
- Gwamnatin Tinubu ta sake cire faretin sojoji daga bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, karo na biyu a jere
- Ba a bayyana dalilin rashin faretin ba, duk da cewa jami’an soja da ake zargi da shirya juyin mulki suna fuskantar shari’ar soja
- A 2026, bikin ya kunshi addu’o’in addini, lacca da jawabin Tinubu, yayin da gwamnati ba ta danganta rashin faretin da batun tsaro ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 66 tun bayan samun 'yancin kai wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
A karo na biyu a jere, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ki yin faretin sojoji da aka saba daga bikin ranar ’yancin kan Najeriya.

Source: Facebook
Wannan mataki ya bar tambayoyi kan dalilin da ya sa ba a dawo da faretin ba, duk da cewa gwamnati ta tabbatar da binciken zargin shirya juyin mulki, cewar Daily Trust.
Gwamnati ta tabbatar da cewa an gano wasu jami’an soja da ake zargi da shirya juyin mulki, kuma suna fuskantar shari’a a gaban hukumomin soja.
A shekarun baya, bikin ranar 1 ga Oktoba ya kan ƙare da faretin sojoji, girmamawar jami’ai, atisayen sojoji da sauran bukukuwan ƙasa.
Sai dai shirin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai na wannan shekara bai ƙunshi faretin sojoji ba.
Maimakon haka, gwamnati ta sanar da bikin da ba shi da hayaniya sosai, wanda ya ƙunshi ibadun addini, lacca ga jama’a da jawabin shugaban ƙasa ga ’yan Najeriya.
Matakin ya zo ne duk da cewa an gudanar da cikakken faretin sojoji a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar 1 ga Oktoba 2024.
A wancan lokaci, Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da sauran manyan baki sun kalli atisayen sojoji da faretin.
An kuma gudanar da sauyin jami’an tsaron girmamawa a matsayin wani ɓangare na bikin ranar ’yancin kan ƙasar.
Sai dai faretin bai kasance cikin shirin bikin 2025 ba, bayan da gwamnatin tarayya ta sanar a ranar 29 ga Satumba cewa ta soke shi.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci
A lokacin, gwamnati ba ta bayar da cikakken bayani kan dalilin soke faretin ba, sai dai ta ce hakan ba zai rage muhimmancin bikin ba.
Soke faretin ya faru ne a daidai lokacin da aka kama wasu jami’an soja bisa zargin da daga baya ya koma binciken yunkurin kifar da gwamnati.
Sai dai sojojin sun musanta cewa akwai alaƙa tsakanin abubuwan biyu a wancan lokacin.
A watan Oktoban 2025, Hedikwatar Tsaron Najeriya ta musanta rahotannin cewa an soke faretin ne saboda wani yunƙurin juyin mulki.
Ta ce an ɗauki matakin ne domin bai wa Tinubu damar halartar wani muhimmin taron diflomasiyya a wajen ƙasar.
Hedikwatar ta kuma ce hakan zai bai wa jami’an tsaro damar ci gaba da ayyukansu na yaƙi da ta’addanci, tayar da ƙayar baya da ’yan bindiga.
Tinubu ta fadi nasarorin da ya samu
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan sauye-sauyen tattalin arziki, bayan shekaru uku da rabi da gwamnatinsa ta fara gyare-gyare.
Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da sama da kashi huɗu cikin 2026, yayin da satar mai da hauhawar farashi suka ragu sosai.
Tinubu ya ce lokacin gyaran tattalin arziki na gaggawa ya wuce, inda gwamnati yanzu za ta mayar da hankali kan samar da wadata ga jama’a.
Asali: Legit.ng
