Iyalin El Rufai Sun Yi Magana kan Wasikar da Aka Ce Ya Aika wa Jam’iyyar ADC

Iyalin El Rufai Sun Yi Magana kan Wasikar da Aka Ce Ya Aika wa Jam’iyyar ADC

  • Iyalan Malam Nasir El-Rufai sun bayyana cewa wasikar da ke yawo da sunan tsohon gwamnan zuwa ga ADC ta bogi ce
  • Mohammed Bello El-Rufai ya tabbatar da cewa rubutun hannun da sakon dake cikin wasikar ba na mahaifinsa ba ne
  • Iyalan sun yi kiran a yi watsi da wasikar wanda suka bayyana a matsayin kokarin haifar da rudani a tsakanin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun nesanta kansu da wata wasika da ke yawo a halin yanzu.

An ga wata wasika a shafukan sada zumunta wadda ake zargin tsohon gwamnan ne ya aika wa shugabannin jam'iyyar ADC na kasa.

El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da 'dan takaran ADC, Isa Ashiru Kudan Hoto: @IsaAshiruKudan
Source: Twitter

Iyalan Nasir El-Rufai sun fitar da jawabi

Punch ta rahoto cewa iyalan tsohon gwamnan sun bayyana cewa wasikar ta bogi ce, an fitar da sanarwar ne a yammacin ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kotu ta raba gardama, ta faɗi sahihin ɗan takarar gwamnan ADC a jihar Ogun

A sanarwar da dan tsohon gwamnan, Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan, ya tabbatar da rashin ingancin wasikar.

Mohammed Bello El-Rufai a shafin X ya tabbatar da cewa wasikar ba daga mahaifinsa ta fito ba.

El-Rufai yana tare da 'dan takaran ADC?

Wasikar da ke dauke da kwanan watan 14 ga Yuli, 2026, tana kalubalantar ‘dan takarar gwamnan Kaduna na jam'iyyar ADC a 2027.

An yi kokarin nuna Nasir El-Rufai bai tare da takarar Isah Ashiru Kudan, bisa zargin rashin kammala rijistar jam'iyya a yanar gizo.

Takardar ta nuna Isah Ashiru Kudan bai gama rajista ba kafin wa'adin 30 ga Afrilu, 2026, amma ya samu tikitin neman gwamna.

Iyalan sun bayyana cewa rubutun hannun da sakon da ke cikin wasikar ba na El-Rufai ba ne kamar yadda wasu suka nuna alamar tambaya.

Dangin El-Rufai sun ce makiya ne suka kirkiri takardar domin kulla makirci da haifar da rudani a jam’iyyar hamayya ta ADC a Kaduna.

Saboda haka, sun bukaci jama'a da shugabannin jam'iyyar ADC da su yi watsi da ita gabatar da cewa hakan wata damfara ce ta siyasa.

Kara karanta wannan

'Yabon Trump ya nuna aikinmu ya na kyau': Fadar shugaban kasa

Bangaren jawabin iyalin tsohon gwamnan Kaduna

Sakon gaggawan ya yi nuni da mummunan rubutun da ke jikin takardar karyar da aka fitar.

Wasikar take cewa:

"Mummunan rubutu da abin da takardar ta kunsa duk ba su da alaka da Mallam Nasir El-Rufai."
Wasikar bogi ta sake nuna wani yunkuri ido rufe na abokan gaban malam wadanda suke neman kawo rudani da rabuwar kai. Ya kamata a yi watsi kuma a yi tir da wannan karya cikin siyasa da suke yi.

Jawabin iyalin tsohon ministan na birnin Abuja ya ce ya kamata wadanda suka kitsa wannan danyen aiki su ji kunyar abin da suke yi.

Likitan Nasir El-Rufai zai je kotu

An samu rahoto ICPC ta shigar da karar Farfesa Bello Abubakar, likitan tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, bisa zargin gabatar da takardun bogi.

Hukumar tana zargin likitan, wanda kwararre ne a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja, da hada baki wajen rubuta rahoton karya, ya gabatar wa kotu.

Ana sa ran shugaban asibitin zai ba da shaida a kotu domin goyon bayan matsayar ICPC cewa an fitar da takardar ba tare da yi wa El-Rufai gwaji ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng