Wata Sabuwa: Rashin Mika Mulki ga Shettima Ya Jefa Tinubu cikin Matsala

Wata Sabuwa: Rashin Mika Mulki ga Shettima Ya Jefa Tinubu cikin Matsala

  • AAC ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana zargin Tinubu da karya Sashe na 145(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya
  • Jam’iyyar ta ce shugaban ƙasa bai aika rubutacciyar sanarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai kafin tafiyarsa ba
  • AAC ta kuma ƙalubalanci Majalisar Tarayya kan zargin rashin ɗaukar matakin ba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa damar riƙe ragamar ƙasa bayan kwanaki 21

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar African Action Congress (AAC) ta kai Shugaba Bola Tinubu, Majalisar Tarayya da Antoni-Janar na Tarayya (AGF) gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Jam'iyyar AAC ta kai karar ne kan zargin cewa shugaban ƙasar bai sanar da Majalisar Tarayya ba kafin tafiya hutun wata guda a Turai.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya duro Najeriya yayin da ake jiran dawowar Tinubu

An kai karar Tinubu gaban kotu
Kashim Shettima na gaisawa tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Jam’iyyar ta shigar da ƙarar ne ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 kamar yadda lauyanta, Inibehe Effiong, ya sanya a shafinsa na X.

AAC ta nemi kotu ta bayyana cewa Tinubu ya karya Sashe na 145(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

AAC ta ce Tinubu ya karya Kundin Tsarin Mulki

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2358/2026, AAC ta ce Tinubu ya bar Najeriya ba tare da aika rubutacciyar sanarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai ba.

Ƙarar ta sanya Shugaba Tinubu, Antoni-Janar na Tarayya, Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da Majalisar Tarayya a matsayin waɗanda ake ƙara.

Jam’iyyar, wadda ta bayar da adireshinta a matsayin House TD7, Global Estate, Apo Primary, Abuja, ta ce Tinubu ya bar Najeriya zuwa Turai ranar 30 ga Agusta, 2026, kuma ya kasance a can har zuwa lokacin shigar da ƙarar.

Kara karanta wannan

MURIC ta gano wurare 2 da Najeriya ta yi 'abin kunya' a taron Majalisar ɗinkin duniya

Jam’iyyar ta nemi kotu ta fassara Sashe na 145

AAC ta nemi kotu ta bayyana cewa bisa tanadin Sashe na 145(1) na Kundin Tsarin Mulki, shugaban ƙasa wajibi ne ya aika rubutacciyar sanarwa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai kafin ya tafi hutu, ko da kuwa tsawon hutun zai kasance nawa ne.

Jam’iyyar ta ce rashin aika irin wannan sanarwa kafin tafiyar shugaban ƙasa “ba bisa tsarin dimokuraɗiyya ba ne” kuma babban take hakkin Kundin Tsarin Mulki ne.

AAC ta ƙalubalanci Majalisar Tarayya

Jam’iyyar ta kuma ƙalubalanci abin da ta bayyana a matsayin gazawar Majalisar Tarayya wajen zama tare da zartar da ƙudurin da zai ba Mataimakin Shugaban Ƙasa damar riƙe ragamar ƙasar bayan Tinubu ya shafe sama da kwanaki 21 yana hutu.

AAC ta nemi kotu ta tabbatar da cewa rashin ɗaukar matakin da Majalisar ta yi ya kasance “ba bisa doka ba, ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki” kuma ya karya aikin da Sashe na 145(2) ya ɗora mata.

Kara karanta wannan

Kungiyar musulmai ta gano wuri 1 da Shettima ya yi kuskure a taron Majalisar ɗinkin duniya

Ta nemi a hana Tinubu sake tafiya ba tare da sanarwa ba

AAC ta kuma nemi kotu ta bayar da umarnin dindindin da zai hana Tinubu sake tafiya hutu a nan gaba, ko cikin Najeriya ko wajen ƙasar, ba tare da ya fara aika rubutacciyar sanarwar da kundin tsarin mulki ya tanada ga Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai ba.

Jam’iyyar ta kuma nemi kotu ta tantance ko fassarar Sashe na 145(1) bisa manufar kundin tsarin mulkin ta ba shugaban ƙasa damar tafiya hutu ba tare da aika rubutacciyar sanarwa ga Majalisar Tarayya ba.

An kai karar Tinubu gaban kotu
Kashim Shettima na jawabi a taron UNGA Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Dalung ya ce Tinubu ya karya doka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da keta tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Dalung ya ce Tinubu ya karya doka ne ta hanyar tafiya hutu ba tare da mika ragamar mulki ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng