Mummunar Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar Kwastam, an Rasa Biliyoyi
- Gobara ta tashi a ofishin Western Marine Command na Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke Apapa, Legas, inda ta lalata dukiya ta miliyoyin naira
- Rahotanni sun ce gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 10:23 na safe sakamakon matsalar wutar lantarki a ɗakin taro
- Sabon Mataimakin Kwanturolan Kwastam, Timothy Jonah, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Gobara ta tashi a ofishin Western Marine Command na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) da ke Apapa, jihar Legas.
Gobarar ta lalata dukiya da ta kai miliyoyin naira a ofishin na hukumar kwastam mai yaki da fasa kwauri.

Source: Original
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 10:23 na safiyar ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 sakamakon tashin wutar lantarki a ɗakin taro na ofishin.

Kara karanta wannan
Amurka ta gode wa Birtaniya da wasu kasashen musulmi 3 kan goyon bayan yaki da Iran
Gobara ta bazu zuwa wasu sassan ginin
Bayan tashin gobarar, jami’an da ke bakin aiki sun yi ƙoƙarin shawo kanta kafin jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas su isa wurin da misalin ƙarfe 10:45 na safe.
Jami’an kashe gobarar sun shiga aikin ceto da kuma ƙoƙarin dakile yaɗuwar gobarar zuwa wasu sassan ginin.
Sabon kwamanda ya ce lamarin abin takaici ne
Sabon Mataimakin Kwanturolan Kwastam, Timothy Jonah, wanda aka tura domin karɓar ragamar jagorancin Western Marine Command daga wanda ya gabace shi, ya bayyana gobarar a matsayin abin takaici.
Jonah ya ce bai daɗe da komawa ofishin ba domin fara aiki kafin gobarar ta tashi.
“Yanzu na dawo bakin aiki domin karɓar ragamar, sai ga shi na fuskanci wannan gobarar,” in ji shi.
Sai dai ya ce duk da mummunan tasirin da lamarin ya haifar, za a iya amfani da shi a matsayin wata dama ta ƙarfafa ayyukan rundunar da kuma matakan kare lafiyar ma’aikata da dukiyoyi.
“Kowane ƙalubale, duk da cewa ba shi da daɗi, wata dama ce ta ƙarfafa ayyukanmu,” in ji Jonah.
Za a binciki musabbabin gobarar
Sabon shugaban ya ce za a kafa wani kwamiti na musamman domin gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, jaridar TheCable ta kawo rahoton.
“A halin yanzu, za mu kafa kwamiti domin binciken musabbabin gobarar,” in ji shi.
Jonah ya kuma yaba wa jami’an da ke bakin aiki bisa gaggawar da suka nuna wajen ƙoƙarin shawo kan gobarar, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas.

Source: Facebook
Gobara ta kona uwa da 'ya'yanta
A wani labarin kuma, kun ji cewa Wata mata da ’ya’yanta hudu sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a gidansu da ke Okochiri, karamar hukumar Okrika a Jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne da safe inda aka gano gawarwakin matar da ’ya’yanta bayan jami’an da suka isa wurin sun tarar da gidan ya kone.
Wani da ya san abin da ya faru, ya ce gobarar ta tashi ne lokacin da wani mutum ke kokarin zuba man fetur a cikin jarka.
Asali: Legit.ng
