Gwamnan Najeriya da ke Biyan Ma'aikatan Shi N500,000 a Wata

Gwamnan Najeriya da ke Biyan Ma'aikatan Shi N500,000 a Wata

  • Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce gonarsa tana biyan ma’aikatan da suka kammala jami’a mafi karancin N500k duk wata
  • Gwamnan, wanda aka fi sani da sha’awar harkar noma, ya ce albashin da yake biyan ma’aikatan gonarsa ya fi abin da wasu ma’aikatan gwamnati ke samu
  • Bago ya kuma bukaci ‘yan kasuwa masu zaman kansu su kara zuba jari a harkar noma domin bunkasa samar da ayyukan yi da tattalin arzikin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa gonarsa tana biyan ma’aikatan da suka kammala jami’a mafi karancin albashi N500k duk wata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Legas yayin bude taron FirstBank na 2026 mai taken “Daga gona zuwa kasuwannin duniya: Gina darajar fitar da kayayyakin Najeriya.”

Kara karanta wannan

Olu Jacobs: Abubuwan sani game da fitaccen jarumin fim da Allah ya yi wa rasuwa

Gwamna Umaru Bago a bakin aiki
Gwamnan jihar Neja a gona. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Gwamna na biyan N500,000

Daily Trust ta wallafa cewa Bago ya bayyana yadda harkar noma, musamman kiwon dabbobi, za ta iya zama babbar hanyar samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya ce albashin da ake biyan ma’aikatan gonarsa ya fi abin da wasu ma’aikatan gwamnati ke samu.

Bago ya ce:

“A gonarmu, muna biyan wanda ya kammala jami’a mafi karancin N500k a wata. Nawa gwamnati ke biya? FirstBank, nawa kuke biya?”

Magana kan ma’aikatan banki

Gwamnan ya ce bambancin albashin yana nuna irin damar da kamfanonin noma masu zaman kansu ke da ita wajen samar da ayyukan yi masu kyau.

Ya yi barkwanci cewa zai iya daukar dukkan ma’aikatan FirstBank da ke samun albashi kasa da N500k ya kai su gonarsa.

Bago ya ce:

“Hakan na nufin zan iya daukar dukkan ma’aikatan FirstBank da ke samun kasa da mafi karancin albashina zuwa gonata.”

Kara karanta wannan

2027: Sabon rikici ya barke tsakanin Wike da gwamnonin APC

Taswirar jihar Niger
Taswirar jihar Niger a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Batun inganta noma

Bago ya bukaci kamfanoni masu zaman kansu su kara shiga harkar noma domin amfana da damarmakin da ke cikinta.

Ya ce:

“Ina son in karfafa gwiwar bangaren masu zaman kansu da su kara yin hakan.”

Gwamnan ya kuma yi gargadin cewa dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje ba abu ne da Najeriya za ta iya ci gaba da yi ba.

Batun shigo da abinci

Bago ya bukaci samar da wata manufa ta kasa da za ta ba da fifiko ga samar da abinci a cikin Najeriya.

Ya jaddada muhimmancin abin da ya kira ‘yancin kai wajen samar da abinci, yana mai cewa lamarin yana da matukar muhimmanci ga kasar.

Gwamnan ya ce Najeriya ta shigo da abinci da ya haura dala biliyan 3 a cikin shekara guda, kuma kudin na iya kaiwa dala biliyan 4 kafin karshen shekarar.

An dakatar da jami'in NSCDC

Kara karanta wannan

Abin da ya sa malaman jami’a 600 a Arewa suke goyon bayan tazarcen Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, bayan mutuwar mutum sama da 30.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yankin M.I. Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar, a safiyar Alhamis.

Tunji-Ojo ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu kuma su ci gaba da bin doka domin a gudanar da binciken cikin gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng