Ba Adalci: Kanawa Sun Yi Martani da Gwamna Ya Raba Filaye, N100m ga Yan Dangwale
- Wasu mazauna jihar Kano sun soki rabon filaye 1,540 da tallafin Naira miliyan 100 da aka bai wa shugabannin ƙungiyar 'yan dangwale
- Sun ce dukiyar gwamnati ta kamata ta amfani al'ummar jihar baki ɗaya ba tare da la'akari da jam'iyya ba kamar yadda su ke zargin an yi
- A nasa bangaren, Shugaban ADC a Kano ya zargi an yi rabon ne domin jan hankalin shugabannin rumfunan zaɓe kafin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu mazauna jihar Kano sun bayyana rashin jin daɗinsu kan matakin Gwamna Abba Kabir Yusuf na raba filaye 1,540 tare da tallafin Naira miliyan 100 ga shugabannin ƙungiyar 'yan dangwale.
Mutanen sun ce matakin ya jawo cece-kuce domin suna ganin ya fifita wata ƙungiya ta siyasa a kan sauran al'ummar jihar.

Source: Facebook
A hira da jarodar Punch, 'daya daga cikin mazauna jihar, Ado Bala, ya ce bai gamsu da yadda aka gudanar da rabon ba, yana mai tambayar dalilin da ya sa ba a yi adalci ga sauran mazauna Kano ba.
Kanawa ba su ji dadi ba
A tatttaunawar ya bayyana cewa dukiyar da aka raba wa yan siyasar ba mallakin mutum daya ba ce, ta jama'ar Kano ce da su ka zabi Abba Kabir Yusuf.
Ya ce:
"Ban ji daɗin rabon filaye da kuɗi ga shugabannin masu goyon bayan APC ba. Shin ƙasar Kano ta APC kaɗai ce?"

Source: Original
A cewarsa, filayen gwamnati mallakin al'ummar Kano ne, kuma gwamna yana riƙe da su ne a madadin jama'a ba tare da bambancin jam'iyya ko ƙabila ba.
Shi ma wani mazaunin jihar mai suna Shehu ya buƙaci gwamnatin jihar ta sake nazarin lamarin, yana mai cewa bai dace a ware irin wannan tallafi ga shugabannin wata ƙungiya kaɗai ba.
Zargin APC kan gwamnatin Kano
A jawabinsa, shugaban jam'iyyar ADC na jihar Kano, Alhaji Musa Ungoggo, ya yi zargin cewa an yi rabon ne domin jawo hankalin shugabannin rumfunan zaɓe kafin zaɓen 2027.
A cewarsa:
"Waɗannan shugabannin su ne ke kula da rumfunan zaɓe, kuma za su iya haɗa kai da jami'an tsaro wajen maguɗin zaɓe."
Ya ce maimakon kashe irin wannan kuɗi, gwamnatin jihar ta fi dacewa ta mayar da hankali kan ilimi da sauran muhimman fannoni.
Ungoggo ya yi ikirarin cewa makarantun firamare da dama na fama da ƙarancin malamai da kayan aiki, yana mai cewa a wasu azuzuwa ana samun ɗalibai sama da 400 da ke bukatar kulawa.
Gwamnan Kano ya raba filaye
A baya, mun kawo labarin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba filaye 1,540 da Naira miliyan 100 ga kungiyar 'yan dangwale ta APC a Kano don karfafa jam'iyya kafin babban zaben 2027.
Bayan ya kaddamar da kungiyar, ya ce su ne ginshikin nasarar APC a zaben da ke tafe, hade da cin nasarar shugaba Bola Tinubu a wa'adi na biyu domin ya dora a kan aikin da ya ke yi wa yan Najeriya.
Mai ba gwamna shawara kan lamuran siyasa Mustapha Hamza Bakwana ya ce suna da karfin kawo kuri'u miliyan daya ga Bola Tinubu a Kano tare da bayar da tabbacin cewa sun gama cin zabe a 2026.
Asali: Legit.ng


