2027: Jigon APC Ya Yi Zargin Kwankwaso na da Dan Takarar Shugaban Kasa ba Obi ba
- Wani jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Iliyasu Musa Kwankwaso ya ce Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su da ƙarfin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Ya yi zargin cewa Rabiu Kwankwaso na iya kasancewa da wata manufa ta siyasa daban duk da kasancewarsa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC
- Musa Iliyasu Kwankwasi ya kuma ce Arewa na ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ayyukan da gwamnatinsa ke aiwatarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani jigo a jam'iyyar APC kuma kakakin kungiyar wadanda gwamantin tarayya ta nada mukamai, Illiyasu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan takarar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce tikitin shugaban ƙasa na NDC, wanda Peter Obi ke jagoranta tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mataimaki, ba shi da ƙarfin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan
Ganduje ya tsokano NDC da Obidents, sun yi masa raddi mai zafi kan taba Obi, Kwankwaso

Source: Facebook
The Sun Nigeria ta kawo labarin cewa Illiyasu ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Laraba 22 ga watan Yuli, 2026.
Kwankwaso ya dura kan takarar NDC
Nigerian Tribune ta wallafa cewa Musa Iliyasu Kwankwaso ya kalubalanci 'yan adawa su bayyana manufofinsu a maimakon kalubalantar Bola Tinubu.
A cewarsa, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su da faɗin tasirin siyasa da goyon bayan da ya mamaye dukkan yankunan Najeriya, wanda zai ba su damar kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen da ke tafe.
Ya ce:
"Wannan shi ne gasa mafi ban dariya da aka taɓa gani a siyasar Najeriya a 'yan shekarun nan."
Ya ƙara da cewa APC na da ƙwarin gwiwar cewa tikitinta zai yi nasara idan aka kwatanta da na NDC da ake ganin ta na kame-kame wajen neman goyon baya.
Illiyasu ya kuma yi zargin cewa Rabiu Musa Kwankwaso na iya kasancewa yana tafiyar da wata dabara ta siyasa duk da kasancewarsa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC.
Zargin jigon APC kan Kwankwaso
A cewarsa, akwai yiwuwar Kwankwaso na goyon bayan wani ɗan takarar shugaban ƙasa daban a ɓoye, yana mai cewa lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.
Da yake magana a madadin mambobin ƙungiyar masu riƙe da muƙaman gwamnatin tarayya, Musa Illiyasu Kwankwaso ya ce sun kuduri aniyar ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyuka da dama da suka amfani Najeriya, musamman a jihohin Arewa.
A cewarsa, shugaban ƙasar ya kamata ya ci gaba da samun ƙwarin gwiwa saboda goyon bayan da yake samu daga Arewacin Najeriya, yana mai cewa Kano da sauran jihohin yankin na tare da shi.
Ya lissafo wasu daga cikin ayyukan gwamnatin da suka haɗa da shirye-shiryen inganta harkar lafiya, kare muhalli, tallafa wa noma da kuma aikin bututun iskar gas daga Abuja zuwa Kaduna da Kano.
Martanin Ganduje ga Kwankwaso
A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan Kano ya yi magana game da nasarar yan takarar NDC, Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa kwankwaso a jihar yayin da zaɓe ke kusantowa.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda tsohon shugaban APC ne a matakin kasa ya yi watsi da fariyar da Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na cewa sun ci zaɓe a Kano idan zaben 2027 ya zo.
Tsohon shugaban ya soki mulkin Obi da Kwankwaso a jihohinsu, inda ya ce ba su yi abin a zo a gani ba har za su nuna wa jama'a domin a fito a kada masu kuri'ar shugaban kasa da mataimaki.
Asali: Legit.ng

