Zargin Cin Kudi Ta Kai ‘Dan Takaran APC a Zaben Majalisa cikin Ragar Hukumar ICPC

Zargin Cin Kudi Ta Kai ‘Dan Takaran APC a Zaben Majalisa cikin Ragar Hukumar ICPC

  • Hukumar ICPC ta tsare dan takarar APC na majalisa a jihar Ekiti, Toyin Okoro, a birnin Abuja kan zarginsa da laifi
  • Ana zarginsa da amfani da kamfaninsa wajen yin kasuwanci da kwangiloli a lokacin da yake kan mukami a majalisa
  • Binciken ICPC ya maida hankali kan karya dokokin aikin gwamnati, ha'inci, da kuma boye gaskiya wajen bada bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jami’an hukumar ICPC masu binciken cin hanci da rashawa a Najeriya sun titsiye Toyin Z. Okoro mai neman takara.

Toyin Okoro yana neman zama ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Ise-Orun/Ikere/Ekiti a jihar Ekiti a zaben 2027.

ICPC.
Shugaban hukumar ICPC a ofishinsa a Abuja, Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN Hoto: ICPC Nigeria
Source: Facebook

Toyin Okoro ya sha tambayoyin jami'an ICPC

Munanan rahotanni da suka fito daga irinsu jaridar The Cable sun nuna ICPC tana tuhumar Majalisar tarayyan da laifin sata.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya fito ya nuna goyon baya ga Tinubu

An gayyaci tsohon hadimin shugaban majallisar tarayya, Rt. Hon. Tajuddeen Abbas zuwa hedikwatar ICPC a Abuja ranar Alhamis.

Tun a ranar 7 ga watan Satumba 2026, ICPC ta rubuta masa takardar gayyata ta hannun jami’inta, Mista Oshinyemi Oluwaseun.

Oluwaseun shi ne shugaban sashen wasu dakaru na musamman, ya gayyaci ‘dan siyasar a madadin shugaban ICPC na kasa.

‘Dan takaran ya isa hedikwatar karfe 2:00 na rana kamar yadda aka yi da shi, bayan jira na mintuna sai aka kai shi dakin tambayoyi.

Hukumar ICPC ta bada belin Toyin Okoro

Jaridar ta ce wasu jami’ai na musamman sun shafe fiye da awanni biyu suna yi masa tambayoyi kafin a bada belin shi da yamma.

Takardun da aka samu sun ce hukumar yaki da cin hanci da rashawan tana zarginsa da ayyukan da suka saba dokar ICPC ta 2000.

A dalilin saba wa sashe na 28 da na 40 na wannan doka aka bukaci ya zo ya sha tambayoyi.

Kara karanta wannan

An fara rade radin kulla sabuwar hadaka domin kifar da Tinubu a 2027

Bayanai sun ce takardar gayyatar ta ba tsohon mai ba shugaban majalisar tarayyan zabin zuwa tare da lauya ko shi da wasu mutanen.

Sahara Reporters ta tabbatar da cewa bayan ya sha tambayoyi har zuwa karfe 5:00, an sake shi da nufin zai sake dawowa nan gaba.

Wani laifi ICPC take zargin ya aikata?

An ce Okoro ya cigaba da amfani da wani kamfaninsa a lokacin kuma yana aiki da shugaban majalisa wanda hakan laifi ne.

An tuhume shi da amfani da matsayinsa a majalisa wajen sama wa kamfanin kwangiloli daga NPA, SMEDAN da NASENI da sauransu.

Wata majiya ta ce da magana ta je gaban ICPC, ya yi karya. Ana zargin ya jawo da takardar murabus dinsa baya don kare kan shi.

Bayan nan ana tuhumarsa da yin karya a rantsuwar da ya yi wa INEC wajen shiga takara. Zuwa yanzu Okoro bai fito ya ce uffan ba.

ICPC.
Hedikwatar hukumar ICPC a birnin Abuja Hoto: ICPC Nigeria
Source: Twitter

Jami'in ICPC ya rasa aiki a dalilin El-Rufai

A baya an ji ICPC ta sallami wani jami'i, Daniel Stephen, bayan na'urar CCTV ta nuna ya taimaka wa matar Nasir El-Rufai ta gan shi.

Kara karanta wannan

An sake rusa lissafin Tinubu, tsohon shugaban Majalisar dokoki ya fice daga jam'iyyar APC

Stephen ya amsa laifinsa na shigar da Aichatou Assabe El-Rufai cikin harabar ICPC ta kofar baya a lokacin da ba na kai ziyara ba.

An zargi matar da mika wa mijinta wata takarda da tattaunawa a kanta na kusan mintuna 15 kafin su fice ba tare da an ankara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng