Ganduje Ya Caccaki Kwankwaso kan Shirin Tattaunawa da 'Yan Bindiga, Ya Fadi Illarsa

Ganduje Ya Caccaki Kwankwaso kan Shirin Tattaunawa da 'Yan Bindiga, Ya Fadi Illarsa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje ya soki daya daga cikin manuofin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kawo a kan tsaro
  • Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa idan yan Najeriya su ka zabe shi da Peter Obi, za a yi kokarin kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar
  • Sai dai Ganduje ya mayar da martani, inda ya ce hanyar da su Kwankwaso ke ganin za ta kawo karshen matsalar za ta karfafa wa yan bindiga ne kawai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa tattaunawa da 'yan bindiga ba ita ce hanyar da ta dace wajen magance matsalar tsaro a Najeriya ba.

Ganduje ya ce duk wata yarjejeniya da ake yi da 'yan bindiga tana ba su damar ƙara samun kuɗi da kayan aiki, lamarin da zai ƙara tsananta matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

2207: Ganduje ya yi wa Obi da Kwankwaso mummunan hasashe, ya hango faduwarsu a Kano

Ganduje ya yi fatali dakalaman Kwankwaso
'Dan takarar mataimakin shugaban kasa a NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Dr. Abdullahi Umar Gnaduje OFR
Source: Twitter

Thisday ta ruwaito cewa Ganduje ya yi wannan bayani ne yayin wani taron manema labarai inda ya mayar da martani ga kalaman ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Abin da ya jawo martanin Ganduje

Jaridar Daily post ta kawo labarin cewa Kwankwaso ya ce shi da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, za su tattauna da 'yan ta'adda idan suka samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Amma Ganduje ya ce:

"Ni ban yarda da tsarin zama da 'yan bindiga domin yin sulhu da su ba."
Gnaduje ya ce akwai illa a gana wa da yan bindiga
Tsohon gwamnan Kano a wani taron siyasa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

Ya bayyana cewa mallakar bindiga ba tare da izini ba laifi ne a Najeriya, saboda haka bai ga yadda za a gayyato ɗaruruwan 'yan bindiga daga daji da makamansu domin su zauna da sarakuna, shugabannin ƙananan hukumomi ko jami'an tsaro domin tattaunawa ba.

Ganduje ya gano gazawa a kalaman Kwankwaso

Kara karanta wannan

'Ko makiyana sun san ni ke da Kano,' Kwankwaso ya yi martani ga Ali Modu Sheriff

A cewarsa, irin wannan tsari ya gaza a baya kuma zai ci gaba da gazawa, domin yana ba masu aikata laifuffuka damar ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Ganduje ya ƙara da cewa idan aka ba su kuɗi, babura da sauran kayan tallafi a matsayin wani ɓangare na sulhu, hakan zai ƙarfafa su su ci gaba da sace mutane domin neman kuɗin fansa da kuma sayen makamai.

Ya ce:

"Ba na ganin wannan dabara ce mai kyau."

Obi, Kwankwaso za su fadi zabe - Ganduje

A baya, kun samu labarin cewa tsohon gwamnan Kano ya yi magana game da nasarar Peter Obi da Rabi'u Musa kwankwaso a jihar yayin da ake shirin gudanar da zaɓe a 'yan watanni masu zuwa.

Abdullahi Umar Ganduje, wanda tsohon shugaban APC ne a matakin kasa ya yi watsi da fariyar da Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na cewa sun ci zaɓe a Kano, domin ko makiyansa sun san ya na da goyon baya.

Tsohon shugaban ya soki mulkin Obi da Kwankwaso a jihohinsu, inda ya ce ba su yi abin a zo a gani ba, wanda ake sa ran shi ne zai iya jawo jama'a su gani, su yaba sannan a jefa masu kuri'a a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng