Za Ta Kwaye wa Kwankwaso, Tsohon Gwamnan Kano Ya 'Amince' Zai Koma APC

Za Ta Kwaye wa Kwankwaso, Tsohon Gwamnan Kano Ya 'Amince' Zai Koma APC

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya, ya amince da komawa jam'iyyar APC bayan ganawa ta sirri
  • Rahotanni sun ce matakin ya biyo bayan rashin samun tikitin Sanatan Kano ta Kudu na jam'iyyar NDC duk da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar gabanin zaben 2027
  • Kabiru Gaya ya taba mulkin Kano tsakanin 1992 da 1993, sannan ya wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa kafin ya rasa zaben 2023 ga Kawu Sumaila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma daya daga cikin jagororin jam'iyyar NDC, Sanata Kabiru Gaya ya gana da shugaban APC, Nentawe Yilwatda.

Sanata Gaya ya amince da komawa jam'iyyar APC bayan wata ganawa ta sirri da Yilwatda a jiya Litinin 20 ga watan Yulin 2026.

Tsohon gwamnan Kano zai koma APC
Nentawe Yilwatda bayan ganawa da Sanata Kabiru Gaya a Abuja. Hoto: Nentawe Yilwatda.
Source: Facebook

Rahotanni daga Channels TV sun bayyana cewa ganawar ta gudana ne a gidan Yilwatda da ke titin Yaounde a Abuja wanda hakan ya jawo jita-jita game da siyasar Kano.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba Kabir ya fadi mutumin da ya lalata siyasar Kwankwaso gaba daya

Ganawar da Gaya ya yi da shugaban APC

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ganawar da aka yi ya shafe kusan mintuna 45 ana tattaunawa wanda ake zargin ya shafi batun sauya sheka bayan rasa tikiti a NDC.

Wata majiya da ta san yadda ganawar ta gudana ta tabbatar cewa Sanata Kabiru Gaya ya amince da komawa jam'iyyar APC bayan tattaunawar da suka yi.

Majiyar ta ce babu shakka Gaya ya amince da komawa APC, lamarin da ake ganin zai sauya yanayin siyasar Kano gabanin babban zaben shekarar 2027. Majiyar ta ce:

"Eh, Sanata Kabiru Gaya ya amince ya koma jam'iyyar APC."

Wannan mataki ya zo ne kwanaki kadan bayan rahotanni sun nuna cewa Gaya ya kasa samun tikitin takarar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin jam'iyyar NDC.

Ana zargin Kabiru Gaya zai koma APC
Shugaban APC yana tattaunawa da Sanata Kabiru Gaya. Hoto: Prof Nentawe Yilwatda.
Source: Facebook

Lokacin da Kabiru Gaya ya mulki Kano

Kabiru Gaya ya fice daga APC a ranar 5 ga Afrilu, sannan ya shiga ADC kafin daga bisani ya koma NDC tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Gaya ya taba zama gwamnan Kano tsakanin shekarun 1992 da 1993 a Jamhuriya ta Uku, sannan ya wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2023.

A zaben shekarar 2023, Gaya ya kasa samun wa'adin komawa Majalisar Dattawa bayan Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP ya doke shi a zaben.

Mutane da dama sun bayyana ra'ayinsu game da yawan sauya shekar Gaya inda wasu ke cewa bai iya zama wuri ɗaya saboda bukatar kansa.

Sanata Kabiru Gaya ya bar jam'iyyar APC

Tun a baya, an ji cewa jam'iyyar APC a Najeriya ta yi babban rashi a jihar Kano bayan ta samu koma baya bayan ficewar wani tsohon sanata daga cikinta.

Sanata Kabiru Gaya wanda ya taba wakiltar Kano ta Kudu ya sanar da yin murabus daga APC a cikin wata wasika da ya aika.

Tsohon sanatan ya bayyana dalilan da suka sanya ya raba gari da jam'iyyar APC wacce ke mulki a tarayyar Najeriya bayan shafe shekaru da dama a cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.