Sabon Minista Nyesom Wike Ya Fara Aiki, An Rugurguza Katafaren Gini a Abuja

Sabon Minista Nyesom Wike Ya Fara Aiki, An Rugurguza Katafaren Gini a Abuja

  • Hukumar FCTA ta fitar da jawabi a game da wani gini da aka ruguza a birnin tarayya na Abuja
  • Mukhtar Galadima ya yi bayanin yadda su ka gano wanda ya mallaki filin da dalilin rusa ginin
  • Jami’an hukumar sun ce wani ne kurum ya kama yin gine-gine a kan filin wani mutumi dabam

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Hukumar FCTA mai kula da birnin tarayya ta bada umarnin ruguza wani tagwayen gini da aka kammala a birnin tarayya da ke Abuja.

A rahoton da aka samu daga Punch, an samu labari an yi wannan gini ne a wani fili da hukuma ba ta bada izini ba, saboda haka aka rusa ginin.

Ginin ya na kan fuloti mai lamba 226 Cad Zone A02 Wuse 1 a unguwar Zone 6 da ke birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Wasu Mutanen Kaduna Sun ba Bola Tinubu Sunan Wanda Su ke So Ya Zama Minista

Sabon Minista
Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Topboychriss
Asali: Twitter

Alhaji Ibrahim Mohammed Kamba da wani Alhaji Ademu Teku ake zargin sun karbe filin, su ka yi wannan gini duk da hukuma ta gargade su a baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Darektan sashen kula da cigaba na FCTA, Mukhtar Galadima, ya ce shi da ma’aikatansa sun yi bincike domin su gano wanda ya mallaki filin.

An yi ta samun sabani game da mallakar, sai a karshe hukumar ta tabbatar da gaskiyar lamarin. Daily Trust ta tabbatar da wannan rahoto a yau.

Babu ruwanmu, dole mu yi rusau - FCTA

Mukhtar Galadima ya shaidawa duniya cewa babu ruwansu da nisan da aka yi a ginin, muddin an sabawa dokoki da ka’idojin birnin tarayyan.

"Mun rushe ginin ne saboda wani ya gina shi ba tare da ainihin takardu da zanen gini ba a kan filin wani mutumi dabam.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Tinubu Ya Nemo Hanyar Sauki, Zai Samar Da Sabbin Gidajen Mai 9,000 Madadin Na Fetur, Bayanai Sun Fito

Bincike ya nuna wanda ya ginin dabam da wanda ya mallaki filin, saboda haka mu ka tunbuke ginin.
Mun kyale ginin ya kawo yanzu ne kafin mu ruguza shi saboda dole mu bi duk matakan. An aika masa takarda ya daina ginin, amma da ya ke ya na da taurin kai, ya cigaba ba tare da jin gargadin da aka yi masa ba.
Bayan bincikenmu, mun gano ainihin wanda aka mallakawa filin, a dalilin haka dole mu cire shi.
Za mu tuntubi sashen shari’armu domin sanin matakin da za mu dauka a kan wanda ya yi ginin.”

- Mukhtar Galadima

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel