Daga karshe, Sanatocin PDP Sun Ziyarci Natasha, Sun Yi Mata Babban Alkawari
- Sanatoci daga jam’iyyun hamayya sun kai ziyara ga Natasha Akpoti-Uduaghan bayan dakatar da ita daga majalisa
- Jagoran tawagar, Seriake Dickson, ya ce yana taron gyaran dokokin haraji a ranar dakatar da ita, don haka bai samu damar halartar zaman ba
- Dickson ya ce majalisa tana da al’adar tallafa wa juna a lokutan wahala, kuma sun yi wa Natasha addu’o’i da shawara don samun mafitar gaggawa
- Dakatarwar Natasha Akpoti ta janyo ce-ce-ku-ce, musamman daga kungiyoyin kare hakkin mata da jam’iyyar PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Wasu sanatoci daga jam’iyyun hamayya sun kai ziyara ga Natasha Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya.
Sanatocin sun ziyarci Natasha ne a gidanta ranar Juma’a 7 ga watan Maris, 2025 bayan dakatar da ita.

Asali: Facebook
Sanatocin PDP sun ziyarci Natasha a gidanta
Tawagar tana karkashin jagorancin Seriake Dickson, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, kamar yadda Sanatan ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta dakatar da Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida bayan da ta ki karbar sabon kujerarta a zauren majalisa.
Takaddamar ta kara kamari bayan da sanatar ta zargi shugaban majalisa, Godswill Akpabio, da cin zarafinta ta fuskar lalata.
Dakatarwar Akpoti-Uduaghan ta haifar da ce-ce-ku-ce da suka daga kungiyoyin kare hakkin mata da kungiyoyin farar hula.

Asali: Twitter
Sanatocin sun yi alkawarin marawa Natasha baya
Sanata Dickson, wanda mamba ne a kwamitin ladabtarwa na majalisa da ya ba da shawarar dakatar da Akpoti-Uduaghan, ya wallafa hoton ziyarar a shafinsa na sada zumunta.
Ya ce an shaida masa cewa zaman jin karar zai gudana ranar Laraba 11 ga Maris, 2025 amma ba a sanar da shi cewa za a yi wani zaman gaggawa ba.
Ya ce:
“A kwanaki uku da suka wuce, na kasance a taron bitar dokokin haraji, wanda ya fara ranar Laraba 5 ga Maris kuma ya kare ranar Juma’a 7 ga Maris.
“Wannan ne dalilin da ya sa ban samu damar halartar zaman kwamitin da ya dakatar da Sanata Natasha ba, an tabbatar min cewa za a saurari karar ranar Laraba.
“Bayan kammala taron, na jagoranci wasu sanatoci na jam’iyyun hamayya zuwa gidan Sanata Natasha, inda muka gana da ita da mijinta."
Dickson ya ce, a matsayinsu na ‘yan majalisa, suna da lokacin farin ciki da kuma lokacin da ake bukatar goyon baya daga juna.
Ya kara da cewa:
“Muna da al’adar tallafa wa juna a irin wadannan lokuta, don haka mun yi addu’a, fatan alheri da shawara don warware matsalar cikin gaggawa.
Natasha: Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki
Kun ji cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta bakin ma'aikatar harkokin mata za ta shiga tsakani da nufin sasanta rigimar shugaban majalisar dattawa da Natasha Akpoti.
Ministar harkokin mata, Imaan Suleiman Ibrahim ta ce za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen sasanta rikicin da ta kira da babban abin takaici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng