‘Yan Takara 2000 Sun Shiga Rudani sakamakon Rigimar cikin Jam’iyyun PDP da LP
- Rikicin shugabanci a jam'iyyun PDP da LP ya saka 'yan takara fiye da 2,098 cikin fargaba rashin makoma
- INEC ta amince ne da bangaren Abdulrahman Mohammed a PDP da na Sanata Nenadi Usman a LP kadai
- Kotu ta yi watsi da karar bangaren Tanimu Turaki bayan sun gama shirya wadanda za su yi masu takara a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - A lokacin da aka fara shirya wa zabe mai zuwa na 2027, wasu ‘yan bangaren jam’iyyun PDP da LP sun shiga cikin rudani.
Akwai bangarori a manyan jam’iyyun siyasar kasar nan wadanda doka ba ta san da zamansu ba don haka da wuya su iya samun takara.

Source: Getty Images
A rahoton Tribune, an fahimci cewa wadanda suka fada cikin ‘yan wadannan zagi ba za a shigar da sunayensu a kan shafin INEC ba.
An fara daura sunayen 'yan takara a INEC
Hukumar zabe ta INEC ta ba jam’iyyun siyasa damar daura sunayen wadanda za su yi masu takarar gwamna da ‘yan majalisa a jihohi.
An bude shafin INEC domin fara wannan aiki ne tun daga Asabar 18 ga watan Yuli kuma za a kammala a ranar Asabar 8 ga Agustan 2026.
Hukumar INEC ta karbi tsagin Abdulrahman Mohammed da na Sanata Nenadi Usman a matsayin halatattun shugabannin PDP da LP.
INEC ta yi watsi da mutanen Turaki da Abure
Saboda haka ne INEC mai gudanar da zabe ta ba wadannan bangarori lambobin sirrin da ake bukata a shafin domin su daura ‘yan takara.
Sai dai a bangare guda, akwai tsagin PDP da ke karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki SAN wanda da alama babu ruwan INEC da ita.
A jam’iyyar adawa ta LP, akwai wani bangare na su Julius Abure da suke da daruruwan ‘yan takararsu.
Mutane fiye da 1,000 za su rasa takarar PDP
Rahoton ya ce su Kabiru Tanimu Turaki sun fito da mutane 993 da ke neman takarar majalisar dokoki da kuma 28 masu neman gwamna.
Tsagin jam’iyyar ta raba masu fam da niyyar su nemi mukamai a zabe mai zuwa amma a yanzu ba a samu damar daura sunayensu ba.
Matakin da INEC ta dauka na aiki da bangaren Nyesom Wike a PDP ya nuna akwai mutane sama da 2, 098 da takararsu ta bi ruwa.

Source: Getty Images
Da aka tambayi mutanen Abdulrahman Mohammed, sun ce tuni sun soma daura sunayen ‘yan takaran PDP a shafin hukumar zabe.
Kakakin PDP na kasa, Jungudo Haruna Mohammed ya ce za su daura sunayen ‘yan takarar gwamna 31 da abokan gaminsu a jihohi.
Baya ga haka suna da mutane kusan 993 da za su nemi Majalisar dokoki a jihohi 36.
Jam'iyyar PDP ba ta gama da shari'a a kotu ba
Mai magana da yawun dayan tsagin na PDP, Kwamred Ini Ememobong ya ce za su daukaka karar da suka rasa a babbar kotun tarayya.
Mutanen Tanimu Turaki sun samu matsala a kotu da Alkali Salim Olasupo Ibrahim ya yi watsi da karar da su Adulphus Wabara suka shigar.

Kara karanta wannan
Rigimar takara tsakanin mutanen gwamnonin APC da shugabannin jam'iyya ta tafi kotu
‘Yan tsagin Wike kuma sun ce babu ruwansu da wadanda suka karbi fam wajen Turaki, suka ce tamkar sun shiga damfarar MMM ne.
Abure: Masu takara a LP sun samu matsala
A LP kuwa, Ken Asogwa ya ce suna da ‘yan takarar gwamna 31 da abokan gaminsu a zaben 2027.
Sakataren yada labaran tsagin Nenedi Usman ya ce sun tanadi mutane 776 da za a daura sunayensu cikin ‘yan takarar majalisar dokoki.
Rigingimun da aka rika yi a jam'iyyar LP
A 2024 aka ji Kwamitin zartarwa na jam'iyyar LP na reshen jihar Edo ya amince da dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure.
Shugabannin jam'iyyar na gunduma da ƙaramar hukumar da ya fito sun dauki matakin sakamakon zarginsa da rashin ɗa'a da zagon ƙasa.
Sakamakon wannan hukuncin, an buƙaci Abure da ya daina ayyana kansa a matsayin ɗan jam'iyyar LP tun daga ranar 24 ga watan Mayu 2024.
Asali: Legit.ng

