Atiku Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa na Gwaji na Tinubu Must Go
- Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun samu kuri’a 80,809, kwatankwacin kashi 73.6, a zaɓen shugaban ƙasa na gwaji da aka yi
- Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun zo na biyu da kuri’a 24,519, wato kashi 22.3, yayin da sauran ‘yan takara suka samu kuri’a 4,471
- Abba Hikima, wanda ya jagoranci zaben, ya ce jimillar mutum 109,799 ne suka kada kuri’a, yana mai cewa za a hada rahoto daga baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Lauya Abba Hikima, wanda ke jagorantar tafiyar Tinubu Must Go (TMG), ya bayyana sakamakon zaben gwaji da aka gudanar kan 'yan takarar da aka fi so a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Abba Hikima ya ce jimillar kuri’a 109,799 aka samu a ƙarshen zaben, inda tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi na jam’iyyar ADC ya samu mafi yawan kuri’un.

Source: Facebook
Atiku ya samu kuri’a 80,809
A sakamakon da Abba Hikima ya fitar a Facebook, Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi sun samu kuri’a 80,809, wato kashi 73.6 na jimillar kuri’un.
Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na NDC sun samu kuri’a 24,519, kwatankwacin kashi 22.3.
Sauran waɗanda aka haɗa ƙarƙashin zaɓin “Others” sun samu kuri’a 4,471, wato kashi 4.1.
Abba Hikima ya ce abin da ya fi ba shi mamaki a zaben shi ne yadda sakamakon ya kasance cikin yanayi mai kama da juna a tsawon lokacin da aka gudanar da shi.
Ya ce bayan kusan mintuna bakwai da fara zaben, Atiku da Amaechi sun kasance da kusan kashi 76.6, yayin da Obi da Kwankwaso ke da kashi 20.9.
Ya ce yayin da adadin masu kaɗa ƙuri’a ke ƙaruwa sosai, adadin ya daidaita tare da ci gaba da kasancewa kusa da yadda yake tun farko.

Source: Facebook
TMG za ta fitar da cikakken rahoto
Abba Hikima ya ce za a fitar da cikakken rahoto kan yadda aka gudanar da zaben, yawan wadanda suka shiga, lokacin da aka kaɗa kuri’a da sauransu.
Ya kuma jaddada cewa duk kuri’a tana da muhimmanci, yana mai cewa har yanzu akwai bukatar haɗin kai da ƙawance tsakanin masu kaɗa ƙuri’a.
APC ta soki Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta gargadi ‘yan Najeriya kan zaɓen Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tana zarginsa da alaƙa da wasu tsofaffin batutuwan cin hanci da rashawa.
Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Felix Morka, ya ambaci batutuwan da suka shafi aikin wutar lantarki na Mambilla, badakalar Siemens, shari’ar William Jefferson da sauransu.
Sai dai zarge-zargen na APC ne, yayin da Atiku ya ƙi amincewa da yadda ake danganta shi da laifin cin hanci, musamman batun Mambilla, inda mai magana da yawunsa ya ce ba gaskiya ba ne.
Asali: Legit.ng

