Fetur Zai Wadatu a Najeriya bayan Sabon Matakin da NMDPRA Ta Dauka

Fetur Zai Wadatu a Najeriya bayan Sabon Matakin da NMDPRA Ta Dauka

  • NMDPRA ta amince da shigo da tan 830,000 na fetur zuwa Najeriya a zangon karshe na shekarar 2026 domin ƙarfafa samar da man fetur
  • Kamfanonin Matrix Energy, AA Rano, AYM Shafa, NIPCO, Pinnacle Oil da Bono Energy sun samu lasisin shigo da fetur
  • Amincewar ta zo ne yayin da matatar Dangote ke ci gaba da adawa da lasisin shigo da fetur da NMDPRA ke bai wa wasu ’yan kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar NMDPRA ta amince da sababbin lasisin shigo da fetur zuwa Najeriya a watanni uku na karshen shekarar 2026.

Wata majiya a hukumar ta tabbatar da cewa NMDPRA ta amince da shigo da tan 830,000 na man fetur a cikin watannin Oktoba zuwa Disamba.

NMDPRA ta bayar da lasisin shigo da fetur
Shugaban hukumar NMDPRA a waje taro Hoto: @NMDPRA_official
Source: Twitter

Majiyar ta sanar da jaridar TheCable cewa adadin ya shafi Premium Motor Spirit (PMS), wato man fetur da ake amfani da shi wajen tafiyar da motoci da sauran ababen hawa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sauya dabara, ta cafke kasurgumin jagoran 'yan ta'adda

Kamfanoni shida sun samu lasisin shigo da fetur

Rahoton S&P, wanda ya fara wallafa labarin bayar da lasisin ranar Litinin, ya ce NMDPRA ta ba kamfanonin dillalan man fetur shida damar shigo da jimillar tan 830,000 a zangon huɗu.

Rahoton ya ce matakin na zuwa ne yayin da gwamnati ke ƙoƙarin ƙara samar da man fetur a Najeriya, musamman saboda matsin lambar da ake samu a kasuwar man fetur ta duniya.

Kamfanonin da suka samu lasisin sun haɗa da Matrix Energy, AA Rano, AYM Shafa, NIPCO, Pinnacle Oil da Bono Energy.

S&P ta ce adadin man da aka ba wa waɗannan kamfanoni lasisin shigo da shi ya yi daidai da rabon da aka yi musu a watan Yuni na zangon uku na shekarar.

Matatar Dangote na adawa da shigo da fetur

Sabon matakin na NMDPRA ya zo ne a daidai lokacin da matatar Dangote ke ci gaba da nuna adawa da lasisin shigo da fetur da hukumar ke bai wa wasu ’yan kasuwar man fetur.

Kara karanta wannan

An fito da babban dalilin EFCC na ayyana neman Abdulrasheed Maina ruwa a jallo

A ranar 25 ga Maris, NMDPRA ta sassauta wasu takunkumin da aka sanya kan shigo da fetur, inda ta bai wa wasu ’yan kasuwar cikin gida sababbin lasisin shigo da man.

Bayan watanni biyu, matatar Dangote ta shigar da sabon ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

A ƙarar, matatar ta kalubalanci lasisin shigo da man fetur da NMDPRA ta bai wa ko ta sabunta wa wasu ’yan kasuwar man fetur.

Shigo da fetur ya ƙaru

Bayanan NMDPRA da aka fitar a ranar 25 ga Agusta sun nuna cewa samar da fetur a cikin gida ya ragu zuwa lita miliyan 25.8 a kowace rana a watan Yuli.

A gefe guda kuma, shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ƙaru zuwa lita miliyan 19.7 a kowace rana a wannan lokacin.

A ranar da ta biyo baya, matatar Dangote ta ce ƙarin shigo da man fetur daga ƙasashen waje na tilasta mata fitar da wasu kayayyakin man fetur da ta samu rarar su zuwa ƙasashen waje.

Matatar ta ce tana da ƙarfin samar da isasshen man fetur da zai biya bukatun Najeriya na cikin gida.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau

NMDRAa
Shugaban hukumar NMDPRA na jawabi a wajen taro Hoto: @NMDPRA_official
Source: Twitter

Farashin fetur na iya kai N5000

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi gargadin cewa farashin man fetur na iya tashi zuwa N5,000 kan kowace lita.

Adewole Adebayo ya yi gargadin cewa farashin fetur na iya kai hakan ne idan Shugaba Bola Tinubu ya samu wa’adi na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng