Kalaman Kwankwaso game da Rashin Tsaro Ya Yi wa APC Zafi, An Yi Masa Martani
- Jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC ta yi watsi da sukar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnatin Bola Tinubu kan tsaro da tattalin arziki
- Jam'iyyar ta ce kalaman Kwankwaso na neman goyon bayan siyasa ne kafin zaɓen 2027, amma babu kamshin gaskiya a dukkanin sukar da ya yi
- Sai dai kakakin Kwankwasiyya ya kara karfafa kalaman Kwankwaso, inda ya dage cewa gwamnati ta gaza kare rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam'iyyar APC mai mulki ta mayar da martani kan kalaman ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya tayar da kura bayan ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.
A wata hira da gidan talabijin na Channels, Kwankwaso ya ce gwamnatin APC ta gaza kare rayukan 'yan Najeriya tare da magance hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arziki.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan Kano ya ce yawan kashe-kashe da ake samu a sassan ƙasar ya nuna akwai buƙatar 'yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen kawo sauyi.
APC ta yi martani ga Kwankwaso
Sai dai a hira da BBC Hausa Daraktan Yaɗa Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya ce waɗannan kalamai ba komai ba ne illa yunƙurin neman goyon bayan jama'a kafin babban zaɓe.
Ya ce:
"Dukkannin abubuwan da Kwankwaso ya faɗi da ma sukar da ya yi wa manufofin jam'iyyarmu, ai ya yi gwamna har sau biyu, sannan ya yi ministan tsaro, don haka ya san matsalar tsaro."

Source: Facebook
Bala Ibrahim ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta kasance tun lokacin da Kwankwaso yake riƙe da muƙaman gwamnati, yana mai cewa:
"Idan da a ce su Kwankwason sun yi wa tufkar hanci, ma'ana sun magance matsalar tsaron a lokacin da suke da shugabanci, don daga hannunsu muka ƙwaci mulki saboda rashin iyawa."

Kara karanta wannan
Ganduje ya caccaki Kwankwaso kan shirin tattaunawa da 'yan bindiga, ya fadi illarsa
Kwankwasiyya ta yi martani ga APC
Ya kuma kare matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka, yana mai cewa duk lokacin da aka bullo da gyare-gyare akwai masu anfani da tsohon tsarin da ke ƙoƙarin hana su yin nasara.
A cewarsa, wasu na zuga jama'a kada su goyi bayan sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa saboda suna cin moriyar matsalolin da ake ƙoƙarin warwarewa.
Sai dai ƙungiyar Kwankwasiyya ta ce tana nan kan matsayinta cewa gwamnatin tarayya ba ta cika babban nauyin da ke kanta ba.
Kakakin ƙungiyar, Dakta Habibu Saleh Mai Lemo, ya ce babban aikin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya ce:
"Duk wani ɗan Najeriya a yanzu zai tabbatar da cewa a yanayin da ake a yanzu a kowane ɓangare na ƙasar an tabbatar da cewa akwai gazawa daga gwamnatin Tinubu, kuma duk ɗan Najeriya na da haƙƙin sanin abin da ke faruwa a ɓangaren tsaro."
Tsohon shugaban APC ya dura kan Kwankwaso

Kara karanta wannan
2207: Ganduje ya yi wa Obi da Kwankwaso mummunan hasashe, ya hango faduwarsu a Kano
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya soki daya daga cikin manuofin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kawo a kan tsaro idan su ka yi nasara a 2027.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa idan yan Najeriya su ka zabe su a yi kokarin kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar ta hanyar tattauna wa da kowa, har da yan bindiga.
Sai dai Ganduje ya mayar da martani, inda ya ce hanyar da su Kwankwaso ke ganin za ta kawo karshen matsalar za ta karfafa wa yan bindiga da kudi, babura da sauran makaman da za su ci gaba da ta'addanci ne.
Asali: Legit.ng
