Kaduna: Ana Zargin An Nadi Muryar Isa Ashiru Yana Caccakar El Rufai a Wayar Tarho

Kaduna: Ana Zargin An Nadi Muryar Isa Ashiru Yana Caccakar El Rufai a Wayar Tarho

  • Ana zargin an nadi muryar Isa Ashiru Kudan yana wasu maganganu marasa dadi a wayar salula game da Nasir El-Rufai
  • Magoya bayan ‘dan takarar gwamnan sun ce babu mamaki makiya ne suka yi amfani da fasahar AI wajen kirkirar sautin
  • Wata matar Nasir El-Rufai ta shaida wa al’umma a jihar Kaduna cewa Isa Kudan za su mara wa baya a zaben gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - An nadi wani sauti da ake zargin an ji ‘dan takaran PDP a zaben gwamnan jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan yana wasu maganganu.

Ana zargin cewa sautin ya nuna Hon. Isah Ashiru Kudan yana yin wasu maganganu da mutanen Nasir El-Rufai sam ba za su ji dadinsu ba.

Isa Ashiru
Isa Ashiru tare da Nasir El-Rufai da matarsa a Kaduna Hoto: Isa Ashiru Kudan/Aisha Ummi Garba El-Rufai
Source: Getty Images

Isa Ashiru: Iyalan El-Rufai sun ji sun gani

Amma duk da haka, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mai dakin tsohon gwamnan, Aisha El-Rufai ta nuna suna nan tare da ‘dan takaran na ADC.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar gwamna a PDP bai son tazarce ya ce wa’adi 1 rak ya ishe shi

Aisha El-Rufai wanda tana cikin matan tsohon gwamnan na Kaduna ta yi amfani da shafinta na Facebook tana nuna wanda take goyon baya.

“Babu gudu, babu ja da baya. Shure-shure bai hana mutuwa.”

Aisha El-Rufai ta ce ko Isa Ashiru Kudan zai casa duka iyalin El-Rufai ne ba shi tsohon gwamnan kadai, ba su goyon bayan tazarcen mulkin APC.

Sakon nata ya nuna ba za su mara wa Uba Sani baya a zaben 2027 duk da ana zargin ‘dan takaran ADC bai tare da El-Rufai tsakani da Allah.

Sautin Isa Ashiru da ake zargin ya fita

A faifen da Legit Hausa ta saurara, ana zargin cewa Isa Kudan ya fada wa wani a wayar tarho cewa saboda ya samu tikiti ne kawai ya shiga ADC.

Idan da gaske muryar shi ce, ‘dan siyasar ya kuma caccaki El-Rufai, yana nesanta kan shi da tsohon gwamnan da yake cewa ya zalunce shi a baya.

‘Dan takaran har ya kara da cewa zaluncin da Malam El-Rufai ya yi a baya ne yake bin shi, a karshe yanzu ya shafe kwana da kwanaki yana tsare.

Kara karanta wannan

Kiran da Sheikh Maqary ya yi wa mabiya darika a jami'a a rigimar wazifa da ATBU

Isa Ashiru Kudan
'Dan takaran ADC a zaben gwamnan Kaduna, Isa Ashiru Kudan tare da mutane a Kaduna Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

'Yan APC suna tare da Isa Ashiru Kudan

Amma wani jagora a ADC kuma mutumin Isa Ashiru Kudan ya karyata zargin, ya ce sautin da ake yawo da shin a bogi ne da wasu suka kirkira.

Duk da ya ce bai da hurumin magana, ‘dan siysar ya ce an kirkire shi ne da nufin a bata gwaninsu.

A matsayinsu na ‘ya ‘yan jam’iyya, ya bayyana cewa sun yi zama kuma aka tabbatar da cewa kowa a ADC yana tare da ‘dan takaran gwamnan.

Sannan kuma za a sake yin wani zama da nufin a tabbatar da matsayar mutanen El-Rufai, amma dai har yanzu Isa Ashiru bai ce uffan ba tukuna.

Hadimin Isa Ashiru ya ki yin magana

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani da yake kamar hadimi a wajen Isa Ashiru Kudan, amma ya yi gum yake cewa ba za su sake magana kan batun ba.

Matashin 'dan siyasar ya ce aikin da ke gabansu shi ne tallata Ashiru Kudan da APC a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu na raɗe raɗin haɗin kai da Kwankwaso da takarar Ganduje a NDC

"An riga an yi martani game da lamarin ba, ba za mu kara cewa komai ba.
"Abin da yake gabanmu yanzu shi ne yaki neman zabe da tallata mai gidanmu dare da rana."

- Inji shi

Kwankwaso zai hade da Ganduje a NDC?

Ana kishin kishin din hadewar Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso a NDC har da samun takarar Sanatan yankin Kano ta Arewa.

Tun da Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya zama gwamna a Kano, aka samu sabani tsakaninsa da magabancin nasa wanda suke tare tun a 1999.

Tsohon kwamishina ya tanka rade-radin haduwar Kwankwaso da Ganduje, yake cewa idan ta tabbata, to karshen tsohon mai gidansa sa ne ya zo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng