An Kashe Bakin Tsanya, Kudan da aka 'Nadi Muryarsa' Ya Gana da El Rufa'i da ke Hannun ICPC

An Kashe Bakin Tsanya, Kudan da aka 'Nadi Muryarsa' Ya Gana da El Rufa'i da ke Hannun ICPC

  • Ana tsaka da maganganu kan wni sautinmurya da aka nada na Isa Ashiru Kudan game da Nasir El-Rufa'i, an hango 'dan takarar gwamnan a ICPC
  • An rika cece-kuce a kan zargin Kudan ya yi wa Nasir El-Rufa'i tas a wani sautin murya, inda ya ce yana tare da tsohon gwamnan saboda tikitin takara
  • Amma dan takarar gwamnan na ADC ya ce ganawar ta kara masu kwarin gwiwar tunkarar zaben 2027 a Kaduna duk da kotu ta hana balin El-Rufa'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Dan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan, ya gana da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmed El-Rufai.

Tattaunawarsu ta zo a daidai lokacin da ake ta ce-e-kuce game da wani sautin murya da aka ce yana da alaka da shi, inda ya caccaki tsohon Kudan ya soki tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

PDP ta yi kaca kaca da gwamnatin Gombe kan zargin bai wa mawakin Kano N315m

Kudan ya gana da El-Rufa'i
Isa Ashiru Kudan tare da tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i da wasu makusantansu Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa da cewa Kudan ya tabbatar da cewa ya gana da El-Rufai, sai dai bai bayyana inda aka gudanar da ganawar ba.

Kudan ya gana da El-Rufa'i

Trust TV ta kawo labarin cewa sanawar ta zo ne bayan wani sautin murya da aka yada a kafafen sada zumunta, wanda aka ce na dan takarar gwamnan ADC ne, ya haddasa muhawara a cikin jam'iyyar.

Sai dai magoya bayan Isa Ashiru Kudan sun yi watsi da sautin, suna mai cewa an kirkire shi ne domin bata masa suna. Haka kuma magoya bayan El-Rufai sun sake jaddada goyon bayansu ga tsohon gwamnan duk da wannan cece-kuce.

A wani bangare kuma, Aisha El-Rufai, matar tsohon gwamnan Kaduna, ta fito fili ta bayyana cewa tana goyon bayan takarar Isa Ashiru a karkashin jam'iyyar ADC.

ADC ta shirya kifar da APC - Kudan

Da yake karin haske kan ganawar, Isa Ashiru ya ce tattaunawar da suka yi da Nasir El-Rufai ta kara masu kwarin gwiwa da hadin kai yayin da suke shirin fuskantar zaben gwamnan jihar Kaduna na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

Kudan ya fadi abin da suka tattauna da El-Rufa'i
Isa Ashiru Kudan tare da Nasir El-Rufa'i Hoto: Isa Ashiru Kudan
Source: Facebook

Ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta shirya tsaf domin kalubalantar gwamnatin APC a jihar, wacce ya zarga da gaza cika alkawuran da ta daukar wa al'ummar Kaduna.

A cewarsa, ganawar ta tabbatar masu cewa lokaci ya yi da za a hada kai domin dawo da adalci, ci gaba da mutuncin al'umma a jihar.

Isa Ashiru Kudan ya ce ADC ba wai kawai ta shirya shiga zabe ba ne, har ma tana da karfin da za ta kayar da gwamnatin APC a Kaduna.

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin mai ci ta gaza magance matsalolin da suka addabi jama'a, yana mai cewa al'ummar jihar sun gaji da wahalhalu da kuma uzurorin da ake bayarwa.

A halin yanzu dai, Nasir El-Rufai na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) bisa zargin aikata rashawa a lokacin da yake gwamnan jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

An nadi 'muryar' Kudan kan El-Rufa'i

A baya, mun kawo labarin ana zargin an nadi muryar Isa Ashiru Kudan yana wasu maganganu marasa dadi a wayar salula game da Nasir El-Rufai, inda magoya bayan ‘dan takarar gwamnan sun ce babu mamaki aikin makiya.

Magoya bayan sun bayyana cewa sun yi amfani da fasahar AI wajen kirkirar sautin. Amma a gefe guda matar Nasir El-Rufai ta shaida wa al’umma a jihar Kaduna cewa Isa Kudan za su mara wa baya a zaben gwamna mai zuwa.

Amma wani jagora a ADC kuma mutumin Isa Ashiru Kudan ya karyata zargin, ya ce sautin da ake yawo da shin a bogi ne da wasu suka kirkira tare da neman jama'a su yi watsi da duk irin wadannan maganganu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng