ADC Ta Nemi Gwamnati Ta Fito da Bayanai kan Yadda aka Kashe N17.5tr a NNPCL

ADC Ta Nemi Gwamnati Ta Fito da Bayanai kan Yadda aka Kashe N17.5tr a NNPCL

  • Jam'iyyar hamayya da ADC ta ce rahoton binciken kudin NNPCL na shekarar 2024 ya haifar da tambayoyin da gwamnati ba za ta iya kauce masu ba
  • Jam'iyyar ta bukaci a bayyana yadda aka kashe har N17.5 tiriliyan kan tsaron makamashi da sauran kudaden da aka batar a bangaren man fetur
  • ADC ta nemi Tinubu, NNPCL da Majalisar Tarayya su wallafa cikakken bayanin kudaden da aka kashe tun daga 2023 zuwa yanzu domin yan Najeriya na da hakki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam'iyyar ADC ta ce ta yi nazari kan alkaluman da ke cikin rahoton binciken kudin Kamfanin Man Fetur na Najeriya na shekarar 2024, tana mai cewa bayanan sun tayar da tambayoyin da ba za a iya yin watsi da su ba.

Kara karanta wannan

2027: Kwankwaso ya fadi yadda shi da Obi ke shirin magance rashin tsaro

Kakakin jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce alkaluman da ke cikin rahoton suna bukatar gwamnatin APC karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi cikakken bayani.

ADC ta caccaki Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu, Bolaji Abdullahi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Mallam Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Jam'iyyar hadakar yan adawa ta bayyana matsayarta ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Bolaji Abdullahi ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata 21 ga watan Yuli, 2026.

Jam'iyyar ADC ta dura kan Bola Tinubu

Bolaji Abdullahi ya ce a baya, 'yan Najeriya sun yi muhawara kan kwangilar sa ido kan bututun mai da ta kai kusan Naira biliyan 48.

Amma yanzu rahoton binciken kudi ya nuna an kashe Naira tiriliyan 7.13 da sunan tsaron makamashi a shekarar 2024.

Ya ce:

"Wadannan alkaluma sun tayar da tambayoyin da gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu ba za ta iya yin watsi da su ba."

Ya kara da cewa idan aka hada sauran kudaden da suka shafi man fetur da kuma basussukan da ke cikin rahoton, adadin ya kai kusan Naira tiriliyan 17.5.

Bolaji Abdullahi ya zargin cewa ana almubazzaranci
Bolaji Abdullahi, kakakin ADC na kasa Hoto: Mallam Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Bolaji Abdullahi ya ce:

"'Yan Najeriya sun cancanci sanin abin da ya jawo wannan gagarumin karin kashe kudi, kuma mafi muhimmanci, abin da kasar ta samu a madadinsa."

Kara karanta wannan

ADC ta fadi yadda za ta kawo karshen mulkin Tinubu a 2027

ADC na zargin an yi almubazzaranci

Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyyar hadakar adawa ta amince cewa kare bututun mai da sauran muhimman kadarorin makamashi wani muhimmin aiki ne na kasa, amma hakan bai kamata ya hana a duba yadda ake kashe kudaden jama'a ba.

Ya ce:

"Yayin da kudin da ake kashewa ke kara yawa, haka kuma wajibi ne gwamnati ta kara bayyana yadda ake kashe su."

Ya kara da cewa a lokacin da iyalai ke fama da tsadar abinci, sufuri da wutar lantarki, kamfanoni ke rufewa, matasa kuma ba sa samun ayyukan yi, 'yan Najeriya na da hakkin tambayar ko tiriliyoyin Nairorin da aka kashe da sunan tsaron makamashi.

2027: ADC na shirin lallasa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana kwarin gwiwar cewa tikitin Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi zai kayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima a babban zaben 2027.

Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce wahalar rayuwa, yunwa da rashin tsaro za su sa 'yan Najeriya su nemi sauyi a 2027, kuma jam'iyyarsu ita ce zabin da za a bukata.

Jam'iyyar ADC ta kuma yi zargin cewa APC na shirin yin magudin zaɓe, amma ta ce al'umma za su kasance cikin shiri domin hana duk wata murdiya da wasu za su yi kokarin yi a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng