Maza 'Yan Daba Sun Shiga Kwartanci Dakunan Dalibai Mata a Taraba

Maza 'Yan Daba Sun Shiga Kwartanci Dakunan Dalibai Mata a Taraba

  • Ɗaliban kwalejin aikin jinya ta jihar Taraba da ke Jalingo sun gudanar da zanga-zanga bayan 'yan daba sun shiga dakin kwanan mata
  • 'Yan daban sun ci zarafin wata daliba gami da yanke mata yatsa guda ɗaya sannan suka sace wayoyi da sauran kayayyaki
  • Ɗaliban sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna bacin ransu da kuma neman gwamnatin jiha ta kawo musu ɗauki kan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Taraba – Ɗaruruwan ɗaliban kwalejin lafiya da ke Jalingo a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar lumana biyo bayan wani hari da aka kai cikin dare a ɗaya daga cikin gidajen kwanan ɗalibai mata da ke wajen makarantar.

'Yan daban an ruwaito cewa sun ci zarafin wata ɗaliba yayin harin sannan suka jikkata ta, har da yanke mata yatsa guda ɗaya.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Dalibai mata a Taraba
Dalibai mata na zanga-zanga Taraba. Hoto: Abdulmumin Imam
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru ne ranar Litinin lokacin da maharan suka shiga cikin gidan kwanan sannan suka kwace wa ɗalibai wayoyinsu da sauran kayayyaki masu daraja.

An kai wadda abin ya faru da ita asibitin GSCN da ke yankin Mile 6 a Jalingo domin yi mata magani, a cewar majiyoyi.

Wani jami'in kungiyar ɗalibai, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaron kansa, ya ce wannan shi ne hari na biyu da aka kai wa gidajen kwanan ɗaliban a cikin makonni biyu.

Ya ce maharan sun kai farmaki wasu gidajen kwanan a makon da ya gabata inda suka sace wayoyi da sauran kayayyaki na ɗalibai.

Matakin da ɗalibai suka ɗauka

A cewarsa, ɗalibai sun shigar da ƙorafi ga hukumomin makarantar bayan harin farko, inda Kwamishinan ilimi ya ziyarci kwalejin sannan ya yi alkawarin inganta tsaro.

"Lokacin da harin farko ya faru a makon da ya gabata, mun kai korafi ga hukumomin makarantar kuma Kwamishinan Ilimii ya ziyarci makarantar ya kuma yi alkawarin za a saka matakan tsaro a duk gidajen kwanan, amma ba a yi komai ba,"

Kara karanta wannan

Rikicin Wike da gwamnonin APC ya isa kasar Faransa, Tinubu zai masu sulhu a can

In ji shi.

Sakamakon haka, ɗaliban sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar makarantar a ranar Litinin, suna bukatar gwamnatin jihar Taraba da hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa domin kare su daga karin hare-hare.

Ɗaliban sun kuma nuna damuwa kan ci gaba da yin amfani da gidajen kwanan da ke wajen makarantar duk da gama gini na gidajen kwanan da ke cikin makarantar.

Taswirar jihar Taraba
Taswirar jihar Taraba a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Jami'in ƙungiyar ɗaliban ya ce makarantar tana da gidajen kwana bakwai — ɗaya na maza shida kuma na mata — amma har yanzu ana saukar da ɗalibai a wajen makarantar.

An sace wayoyin dalibai mata

Harin ya faru ne kwanaki kadan bayan Ma'aikatar Ilimin Kololi ta Jihar Taraba ta ziyarci kwalejin biyo bayan rahoton harin fashi da aka kai wa gidajen kwanan ɗalibai.

Ma'aikatar ta ce mutane ɗauke da makami sun shiga gidajen kwanan, suka sace wayoyi sannan suka ci zarafin ɗalibai.

Ta bayyana cewa an sace wayoyi 33 yayin da wasu ɗalibai suka samu raunuka. An gano wayoyi uku da takobi guda a wurin da lamarin ya faru, a cewar rahoton ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

Shugabar makarantar, Dr Dorcas Dugule, lokacin da aka tuntube ta, ta tabbatar da cewa tana kan magance matsalar amma ta ƙi cewa komai a nan take.

Abdulmumin Imam ya wallafa bidiyon zanga-zangar da daliban suka gudanar a shafinsa na Facebook.

Mutane sun mutu a Taraba

A wani labarin, kun ji cewa aƙalla mutane biyar da ake zargin masu hakar ma'adinai ne ba bisa ƙa'ida ba sun mutu biyo bayan rushewar rijiyar hakar ma'adinai a Taraba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami'in Hulɗa da Jama'a na Ƴan Sanda, ASP Victor Mshelizah, ya ce mutane biyar ne aka fito da su daga rijiyar da ta rushe.

Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin gudanar da bincike a cikin rijiyar domin gano ko akwai sauran masu hakar ma'adinai da suka maƙale a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng