Ana Wata ga Wata: Sabuwar Matsala Ta Kunno kan Trump a Amurka

Ana Wata ga Wata: Sabuwar Matsala Ta Kunno kan Trump a Amurka

  • CNN, MS NOW da Politico sun kai ƙarar gwamnatin Donald Trump domin neman dawo da damar ’yan jaridarsu shiga Fadar White House
  • Kamfanonin sun ce soke izinin shiga na ’yan jaridarsu ba tare da sanarwa ko bin wata hanya ba ya shafi haƙƙinsu na Kundin Tsarin Mulkin Amurka
  • Matakin ya biyo bayan umarnin Trump na hana kafafen shiga Fadar White House, inda ya zarge su da yada abin da ya kira “ƙagaggun labarai da ƙarya”

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - CNN, MS NOW da Politico sun kai ƙarar gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump bayan an hana ’yan jaridarsu shiga Fadar White House tare da soke takardun izinin aikin manema labarai.

Kamfanonin dillancin labaran uku sun sanar da matakin shari’ar ranar Litinin, inda suka ce suna neman a dawo musu da damar shiga Fadar White House tare da kare haƙƙoƙinsu na Kundin Tsarin Mulkin Amurka.

Kara karanta wannan

Trump ya bukaci 'yan Amurka da ke Iran su dauki wani matakin gaggawa

An kai karar Trump kotu
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sun ce za su kare ’yancin manema labarai

A wani rahoto da ABC News ta wallafa ranar Litinin, 21 ga Satumba, ta fara bayyana cewa kafafen uku na shirin shigar da ƙara bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Amurka da ya shafi ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yan jarida.

Sai dai daga baya tashar CNN ta ruwaito cewa CNN, MS NOW da Politico sun shigar da ƙarar a kan gwamnatin Trump a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da CNN, MS NOW da Politico suka wallafa, sun ce sun sanar da gwamnati cewa za su kai ƙarar domin kare haƙƙinsu na kundin tsarin mulki da kuma ƙa’idar cewa gwamnati ba ita ce ke yanke shawarar abin da manema labarai za su wallafa ba.

Trump ya zargi kafafen da yada “ƙarya”

Matakin shari’ar ya biyo bayan shawarar Trump a ranar Juma’a ta hana kafafen uku shiga harabar Fadar White House.

Kara karanta wannan

APC ta yi zarge zarge masu nauyi kan Atiku, ta bukaci ya janye daga takara

Trump ya zarge su da bayar da rahotannin da ya bayyana a matsayin ƙagaggun labarai da ƙarya”, game da shi, gwamnatinsa da kuma Amurka.

Sai dai a sanarwar haɗin gwiwarsu, CNN, MS NOW da Politico sun ce Fadar White House ta soke izinin ’yan jaridarsu ne ba tare da sanarwa ko bin wata hanya ta doka ba, saboda rashin amincewa da rahotannin da suke wallafawa.

Sun ce idan ba a kalubalanci matakin ba, hakan na iya yin barazana ga ’yancin aikin jarida da kuma haƙƙin jama’a na samun labarai masu zaman kansu ba tare da katsalandan daga gwamnati ba.

An kwace katunan shiga Fadar White House

Karar ta biyo bayan sanarwar Trump cewa za a hana kafafen uku shiga harabar Fadar White House.

A ranar Asabar, 19 ga Satumba, an hana ’yan jaridun kafafen uku shiga Fadar White House bayan sanar da dokar hana su shiga.

An kwace katunan izinin shiga na wasu daga cikin ’yan jaridun lokacin da suka yi ƙoƙarin shiga Fadar White House.

An maka Trump kara a kotu
Shugaba Donald Trump na Amurka na jawabi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya samu iko kan Greenland

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, an yi awon gaba da baarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta cimma yarjejeniya da Denmark da Greenland da za ta ba ta ikon dindindin kan tsaro da sauran bukatun Greenland.

Trump ya ce Amurka za ta samu cikakken ikon yin duk abin da ta ga ya dace domin kare tsaron Greenland da na Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng