Alkali Ta Sake Dage Shari’ar El Rufai da ICPC da 'Yan Sanda sai Oktoba
- Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta daga shari'ar Nasir El-Rufai da ICPC, ‘Yan sanda da AGF sai zuwa watan Oktoba 2026
- An yi hakan ne domin ba lauyan El-Rufai damar maida martani ga sabuwar takardar da lauyan Ministan shari’a ya kawo
- Tsohon gwamnan yana kalubalantar samamen da hukumomi suka kai gidansa na Abuja a watan Fubrairu har ya bukaci N1bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wata babbar kotun tarayya mai zama a birnin Abuja ta dage shari’ar da Nasir El-Rufai ya shigar, yana neman diyyar N1bn.
Tsohon gwamnan Kaduna ya yi karar hukumar ICPC, shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma Ministan shari’a na kasa.

Source: Facebook
Nasir El-Rufai sun koma kotu a Abuja
Ranar Litinin labari ya fito daga The Guardian cewa kotun tarayya ta daga ranar sauraron karar da Nasir El-Rufai ya shigar kwanaki.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Sai ranar 27 ga watan Oktoba 2026 ne Mai shari’a Joyce Abdulmalik za ta cigaba da sauraron karar, ta ba lauyoyin mai kara damar martani.
A lokacin ne lauyan Nasir El-Rufai, Akinyemi Aremu zai tanka martanin da lauyan gwamnatin Najeriya ya gabatar gaban kotun.
Lauya ta bukaci karin lokaci a kotu
Yayin da aka ambaci batun, Akinyemi Aremu ya ce kotun ta shirya sauraron lamarin, amma gwamnati ta nemi karin lokaci ta shirya.
Maimuna Lami-Shiru mai kare babban lauyan gwamnati ta nemi a kara mata lokaci domin ta gabatar da nata bayanan da kyau gaban kuliya.
Lauyan tsohon gwamnan da mai kare Shugaban ‘yan sanda, Ezekiel Rimamsomte da lauyan ICPC ba su kalubalanci Lami-Shiru ba.
Malam El-Rufai yana neman diyyar N1bn
Daily Nigerian ta ce ‘dan siyasar yana neman N1bn daga hannun ICPC, IGP da AGF saboda an lalube masa gidansa a birnin Abuja.

Kara karanta wannan
Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC
Oluwole Iyamu, SAN ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/345/2026 a madadin El-Rufai, ya gabatar wa kotu da roko har bakwai.
A ciki, lauyan yana so kotu ta ayyana cewa binciken gidan El-Rufai mai lamba 12 a hanyar Mambilla a Aso Drive a Abuja ya saba dokar kasa.
Iyamu, SAN ya fada wa kotu cewa hakan ya ci karo da adalci, da kuma kiyaye kima da mutuncin El-Rufai a kundin tsarin mulkin Najeriya.
El-Rufai yana so a gagara amfani da abubuwan da aka samu a gidansa daga binciken a matsayin hujjoji a kotu tunda ba a bi ka’ida ba.
Ya kuma nemi alkali ya sa a maida masa kayayyin da aka dauka a gidan. Sai dai hukumar ICPC tana adawa da bukatun a kotun tarayyar.
Lauyoyin hukuma sun ja da bukatar El-Rufai
Lauyan ICPC ya roki a yi watsi da karar haka zalika masu kare Babban lauyan gwamnati (AGF).
‘Yan sanda sun fada wa kotu cewa ba su saba doka ba, suna da hurumin bincike, kamawa ko gurfanar da duk wani wanda ake zargi
Saboda haka Alkali Joyce Abdulmalik ta daga zama sai zuwa karshen watan Oktoba mai zuwa.
Da farko El-Rufai ya hada da Babban alkalin wata kotun majistare a Abuja a shari’ar, amma ya janye saboda gaza gane wanda ake kara.

Source: UGC
Hudubar Sheikh Sanusi Khalil kan El-Rufai
Rahoton nan ya ce Sheikh Sanusi Khalil ya yi ikirarin Bola Tinubu ya ce babu hannun shi a wajen rike Nasir El-Rufai da ake yi har yanzu.
Malamin ya yi kira ga Uba Sani ya yi wa tsohon mai gidansa adalci tunda shugaban kasa ya ce wuka da nama yana hannun gwamnan Kaduna.
Sheikh Sanusi Khalil ya yi maganar Nasir El-Rufai ne a wata hudubar Juma'a da ya gabata kwanan nan.
Asali: Legit.ng
