Haɗakar Su El Rufa'i Ta Yi Babban Kamu a Kaduna, Hon. Isah Ashiru Ya Gindaya Sharadi
- Jam'iyyar haɗaka watau ADC na ci gaba da jan hankalin manyan ƴan siyasa kwanaki kalilan bayan kaddamar da ita a Abuja
- Tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar PDP, Hon. Isah Ashiru Kudan ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin haɗaka don kawo karshen mulkin APC
- Sai dai ya ce yana nan a jam'iyyar PDP amma yana fatan ƙungiyar haɗakar za ta sauya tunani, ta dawo cikin PDP domin tarar wa APC a 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Hon. Isah Ashiru Kudan ya karɓi haɗakar ADC hannu bibbiyu.
Hon. Isah Ashiru ya bayyana cewa zai haɗa kafaɗa da kafaɗa da tawagar haɗaka domin kawar da gwamnatin APC, wacce ba ta damu da kuncin da ta jefa al'umma ba.

Asali: Facebook
Fitaccen ɗan siyasar ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi wacce Aliyu Abubakar Kwarbai ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliyu Abubakar Kwarbai yana cikin jagororin matasan jam'iyyar PDP kuma daya daga cikin magoya bayan Hon. Isa Kudan a jihar Kaduna.
Isah Ashiru ya amince ƴan adawa su haɗa kai
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce zai haɗa kai da haɗakar ADC amma ba zai bar jam'iyyarsa ta PDP ba domin yana tunanin ita ce jam'iyyar da ya dace ƴan adawa su yi amfani da ita.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan haɗakar ƴan adawa karƙashin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ta zabi ADC a matsayin jam'iyyar kifar da APC a 2027.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na cikin waɗanda ke jagorantar wannan tafiya da nufin kawo ƙarshen mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Da yake tsokaci kan wannan ci gaba, ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP a 2023 ya ce zai shiga duk wata haɗaka da aka kafa don kawo ƙarshen mulkin danniya na APC.
Hon. Isah Ashiru Kudan za bar PDP zuwa ADC?
Yayin da aka tambaye shi ko zai fice daga PDP zuwa jam'iyyar haɗaka watau ADC, Hon. Isah Ashiru ya ce:
"A'a muna nan a PDP mai albarka kuma da yardar Allah a wannan zaɓe mai zuwa na 2027, babu wata jam'iyya da za ta iya kauda waɗannan mutanen idan ba an zo an yi haɗaka ba."
"Ina mai tabbatar maka da cewa idan sun gama shirye-shiryensu za su nemi wace jam'iyya ce za su jingina da ita don kayar da wannan gwamnati, PDP za su dawo da yardar Allah."
- Inji Isah Ashiru Kudan.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa PDP a shirye take, za ta karɓi waɗannan ƴan haɗaka domin ceto Najeriya daga gwamnatin APC da ya kira da marasa tausayi.
Isah Ashiru ya ce tawagar haɗaka na fargabar tangal-tangal ɗin da PDP ke yi a sama, inda ya ba da tabbacin cewa saura kiris su shawo kan rikicin jam'iyyar.
ADC ta fara zawarci gwamnoni 5 kafin 2027
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC da gamayyar jagororin adawar Najeriya suka shiga, ta fara zawarcin gwamnoni biyar kafin zaɓen 2025.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jam’iyyar ADC na amfani da rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP ke fama da shi domin jawo wasu gwamnoni.
Wani babban jigo daga jihar Katsina ya ce akwai gwamnoni biyar da suka riga suka bayar da tabbacin za su sauya sheka zuwa ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng