Hadimin Abba Kabir Ya Fadi Mutumin da Ya Lalata Siyasar Kwankwaso Gaba Daya
- Daraktan yada labarai na gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi magana kan siyasar Rabi'u Kwankwaso
- Dawakin Tofa ya zargi Injiniya Buba Galadima da jawo koma bayan siyasar tsohon gwamnan Kano tun bayan hadewarsu
- Ya ce Galadima bai taba kawo gagarumar nasara ga 'yan takarar da ya mara wa baya ba, yana mai kawo misali da Muhammadu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Daraktan Janar na Yada Labaran gwamnan Kano ya fadi wanda ke lalata siyasar Rabi'u Kwankwaso.
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya zargi Injiniya Buba Galadima da kasancewa babban dalilin da ya haddasa koma bayan siyasar tsohon gwamnan Kano.

Source: Twitter
Sanusi Bature ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a gidan rediyo a Kano, wanda jaridar Tribune ta bibiya.
Siyasar Kwankwaso: Hadimin Abba ya zargi Buba Galadima
Dawakin Tofa ya bayyana Galadima a matsayin mutumin da ke manne wa manyan 'yan siyasa domin amfana, yana mai cewa ya dade yana sauya goyon baya ga masu neman shugabancin kasa ba tare da ya samar da wata gagarumar nasarar siyasa ba.
Ya kuma yi zargin cewa kusancin Galadima da Rabiu Kwankwaso ya taimaka wajen durkusar da tasirin siyasar tsohon gwamnan, har ya rika sauya jam'iyyu daga wannan zuwa waccan ba tare da samun ci gaba ba.
Dawakin Tofa ya ce Galadima ya taba gaza taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokutan da yake neman mulki.

Source: UGC
Abin da ya ba Buhari nasara
A cewarsa, Buhari ya samu nasarar lashe zabe ne bayan ya nisanta kansa daga Galadima tare da hada kai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ce hakan ya kai shi ga samun mulki da kuma sake cin zabe.
Ya ce Kwankwaso bai dauki darasi daga wannan lamari ba, yana zargin cewa Galadima na ci gaba da kasancewa kusa da Atiku Abubakar da Bola Tinubu da kuma Kwankwaso a lokaci guda.
Bature ya kuma yi tambaya kan irin tasirin siyasar Galadima, yana mai zargin cewa bai iya gina karfin siyasa a garinsu na Bade da ke Yobe ba, sai dai ya dogara da masu fada a ji a Abuja.
Wadannan kalamai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauya sheka da sabuwar daidaituwar siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027, cewar Da
Zuwa lokacin wallafa rahoton, Buba Galadima bai fito ya mayar da martani kan zarge-zargen ba duba da cewa ya dade yana tare da Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso ya magantu kan zaben Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaida wa shugaba Bola Tinubu da sauran yan Najeriya babban kalubalen da ke tunkaro tikitin takarar APC a 2027.
Sanata Kwankwaso, wanda ke neman kujerar mataimakin shugaban kasa a NDC ya bayyana cewa tikitin Musulm-Musulm zai yi wa Tinubu cikas a zabe mai zuwa.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tsayar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa, amma ya ce akwai mafita.
Asali: Legit.ng

